FIFA: Jerin ‘Yan Wasan da ke Takarar Lashe Kyautar Gwarzon Duniya
Ƴan wasa shida da suka taimaka wa Manchester City lashe kofuna uku a kakar 2022-23 na cikin waɗanda Fifa ta zaɓa domin lashe kyautar gwarzonta na 2023.
Erling Haaland da Julian Alvarez da Kevin de Bruyne da Ilkay Gundogan da Rodri da kuma Bernardo Silva na cikin sahun farko na jerin sunayen ƴan wasan da ke takarar lashe kyautar ta gwarzon duniya na Fifa.
Lionel Messi wanda ya lashe kyautar sau biyu da kuma Kylian Mbappe na cikin jerin sunayen haɗi da ɗan wasan Ingila Declan Rice.
Kocin Manchester City Pep Guardiola na cikin masu horar da ƴan wasa da Fifa ta zaɓa domin lashe kyautar gwarzon koci.
Guardiola na takarar lashe kyautar ne da masu horar da ƴan wasa uku da suka ƙunshi tsohon kocin Celtic Ange Postecoglou da ke jagorantar Tottenham a yanzu.
Messi wanda ya lashe wa Argentina Kofin Duniya shi ke riƙe da kambin.
Sai dai babu Cristiano Ronaldo a cikin jerin masu takarar lashe kyautar wanda ya koma taka leda a kungiyar Al Nassr ta Saudiyya a watan Disamba.
Masana ƙwallon ƙafa ne da suka ƙunshi tsohon ɗan wasan Chelsea Didier Drogba suka zauna suka tantance zaratan ƴan ƙwallon.
Read Also:
Tun a ranar Alhamis da aka sanar da sunayen ƴan wasan Fifa ta buɗe shafin jefa ƙuri’a a shafinta na fifa.com inda za a rufe a tsakiyar Oktoba.
Masu horar da ƴan wasa na ƙasashe da kyaftin kyaftin da ƴan jarida da kuma masoya ƙwallon ƙafa ne za su jefa ƙuri’a domin zaɓen gwarzon ɗan ƙwallon na duniya.
Jerin ƴan wasan da ke takara
Julian Alvarez (Argentina/Man City)
Marcelo Brozovic (Croatia/Al Nassr)
Kevin De Bruyne (Belgium/Man City)
Ilkay Gundogan (Germany/Barcelona)
Erling Haaland (Norway/Man City)
Rodri (Spain/Man City)
Khvicha Kvaratskhelia (Georgia/Napoli)
Kylian Mbappe (France/Paris St-Germain)
Lionel Messi (Argentina/Inter Miami)
Victor Osimhen (Nigeria/Napoli)
Declan Rice (England/Arsenal)
Bernardo Silva (Portugal/Man City)
Masu takarar gwarzon koci
Pep Guardiola (Spain/Man City)
Simone Inzaghi (Italy/Inter Milan)
Ange Postecoglou (Australia/Tottenham)
Luciano Spalletti (Italy/Italy national team)
Xavi (Spain/Barcelona)
Gwarzon mai tsaron raga
Yassine Bounou (Morocco/Al Hilal)
Thibaut Courtois (Belgium/Real Madrid)
Ederson (Brazil/Man City)
Andre Onana (Cameroon/Man Utd)
Marc-Andre ter Stegen (Germany/Barcelona)