Tsofafin ‘Yan Wasan Kwallon Kafa da Suka Rasa Dukiyoyinsu

 

Akwai wasu tsofaffin ‘Yan wasan kwallon da suka tsiyace bayan sun ajiye wasa.

Daga cikin wadanda ritaya ta sa suka tsiyace har da Marigayi Diego Maradona.

Babayaro, Ronaldinho da Royson Drenthe suna cikin sauran da fatara ta kama su.

Legit.ng ta tattaro maku jerin wasu ‘yan wasan kwallon kafa 12 da su kawo ba su da komai a Duniya, bayan sunyi ritaya daga taka leda.

Tsohon ‘dan wasan Super Eagles Celestine Babayaro bayan ya buga wa Chelsea da Newcastle United na Ingila, ya tsiyace a shekarar 2011.

Wani ‘dan kwallon da yanzu bai da arziki shi ne Royson Drenthe wanda ya buga wa manyan kungiyoyin kwallon kafa har da Real Madrid.

Ronaldinho wanda ya taba zama gwarzon Duniya shi ne ya fi ba kowa mamaki a jerin, an yi lokacin da $7 kadai aka samu a bankinsa gaba da baya.

Marigayi Diego Maradona shi ma ya samu kansa a irin wannan mawuyacin hali a shekarar 2009.

1. Diego Maradona (kasar Argentina) – ya tsiyace a 2009.

2. Ronaldinho (Brazil) – £5 rak ke cikin asusun bankinsa a 2020.

3. Royston Drenthe (Holland) – bai da komai a 2020.

4. David James (Ingila) – ya tsiyace a 2015.

5. Asamoah Gyan (Ghana) – £600 suka rage a asusun bankinsa a 2018.

6. Paul Gascoigne (Ingila) – Ana zargin bai da ragowar komai a banki.

7. Celestine Babayaro (Najeriya) – ya tsiyace a 2011.

8. John Arne Riise (Norway) – ya tsiyace tun 2007.

9. Brad Friedel (Amurka) – ya ce ya tsiyace a 2011.

10. Keith Gillespie (A/Ireland) – ya tsiyace a 2010.

11. Eric Djemba Djemba (Kamaru) – ya tsiyace a 2007.

12. Willem Vries (Afrika ta Kudu) – Bai da kudin da zai saye akwatin talabijin.

A 2017 ne ku ka ji cewa Ronaldinho ya yi bankwana da tamola. ‘Dan wasan ya shaida wa jaridar Marca ta kasar Sifen wannen ne bayan ya yanke hukuncin.

Ronaldinho mai shekaru 40 a duniya yayi aiki a matsayin jakada a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, inda ya yi tashe kafin ya tafi AC Milan a Italiya.

Bayan ritayar Ronaldinho ne aka kama fitaccen tsohon ‘Dan wasan Duniyan da fasfon bogi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here