ALLAH ya yi wa ‘Yar Ministan Sadarwa Rasuwa

Allah ya yi wa ‘yar Ministan sadarwa na Najeriya Dakta Isa Ali Pantami rasuwa.

Dakta Pantami ya sanar a shafinsa na Twitter a ranar Litinin cewa ‘yarsa, Aishah Isa Ali ta rasu a Abuja.

Ministan ya kara da cewa saboda wasu uzurori za a yi jana’izarta a ranar Talata a masallacin Annur da ke Abuja.

Aishah Isa Ali (Amal), diyar Ministan Sadarwa ta tattalin arziki na zamani, Shiekh Isa Ali Pantami ta rasu.

Amal wacce ke da shekaru 13 a duniya ta rasu ne a ranar Litinin 23 ga watan Nuwamban 2020 kamar yadda Sheikh Pantami ya sanar ta shafinsa na Twitter.

Ministan ya kuma sanar da cewa za ayi jana’izar ta a gobe (Talata) a masallacin Annur da ke Wuse 2 a Abuja bayan sallar Zuhr idan Allah ya kai mu. Ga sakon da ministan ya wallafa.

“Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Rajiun! “Allah ya yi wa ‘ya ta mai shekaru 13, Aishah Isa Ali (Amal) ta rasuwa ba dadewa ba.

“Saboda wasu uzurori, zai ayi mata sallar jana’iza gobe a masallacin Annur, Wuse 2, da zarar an kammala sallar Zuhr in sha Allah.

“Allah ya gafarta mata, ya jikanta da rahama.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here