Filato: Mutane Sun Kamu da Wata Cuta Bayan Cin Kayan Wawason Tallafin Korona

 

Fiye da mutane 20 sun fadi ciwo a wani kauye da ke jihar Filato.

Bayan jama’an sun sha wani kunu duk suka barke da zawo.

Kuma alamu sun nuna cewa geron da aka yi kunun ne mai matsalar Fiye da mutane 20 sun fadi ciwo a kauyen Joi dake jihar Filato, bayan sun sha wani Kunu da akayi da gero, kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar wa da Premium Times.

Kauyen yana cikin karamar hukumar Riyom da ke jihar Filato. Wadanda cutar ta kama sun hada da dagacin kauyen mai suna Stephen Jugu, wanda ya samu lafiya cikin ranakun karshen mako.

Kamar yadda bayanai suka kammala, an siyo geron ne a hannun wani mai karamin shago a kasuwar anguwar, ranar Talata.

Kamar yadda Jugu, wanda sakataren wata coci ne, ya tabbatar da yadda fiye da mutane 20 suka shiga cikin matsanancin hali bayan sun sha kunun a ranar Litinin.

“Na farka da tsakar dare ina ta zawo, hakan ya cigaba har safiya. Sai na gano ashe saboda wannan kunun da na sha ne.

Sai daga baya na gano duk wadanda muka sha kunu tare sun fuskanci irin hakan.

Kusan mutane 20 ne, amma yanzu duk an sallamesu daga asibiti,” yace.

Shugaban anguwar, wanda ya tabbatar da duk wadannan mutanen sun fadi ciwon, ya ce sun sanar da shugaban bunkasa anguwanni yadda lamarin ya auku

“Sun je sun siyo gero wurin wani mutum mai karamin shago.

Sai wata mata ta hada kunu dashi, ta rabawa ‘yan uwa da abokan arziki. Duk wadanda suka sha kunun sun barke da zawo.

Wasu daga cikinsu har suma suka yi ta yi, wasu suna kashin jini.

“Duk sai da su ka kwanta asibiti, inda aka basu magani,” kamar yadda Tim Danchal, shugaban kungiyar habaka anguwar Jol, ya tabbatar.

Danchal ya ce, har yanzu hukuma tana cigaba da bincike a kan lamarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here