Kashi 5% na ƙananan Yara na Fama da Tarin Fuka a Jihar Kano – Masana
Masana sun koka kan yadda cutar tarin fuka ta yawaita cikin ƙananan yara a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.
Jihar Kano – Kungiyar kula da lafiya ta SFH ta yi taro na musamman kan ciwon tarin fuka a jihar Kano.
Masana lafiya sun tattauna kan yadda tarin fuka ya yawaita tsakanin yara ƙanana a fadin jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar SFH ta bayyana kalubalen da ake fuskanta a jihar kan cutar.
Yawaitar tarin fuka tsakanin yara a Kano
Read Also:
Kungiyar ta bayyana cewa ana samun yaɗuwar cutar tarin fuka a tsakanin yara ƙanana da kashi 5%.
Hakan na nuni da cewa duk cikin yara ƙanana 100 a jihar ana samun yara biyar da ke dauke da cutar.
Wani ma’aikacin jinya, Dakta Ibrahim Umar ya bayyana cewa jihar Kano ce gaba gaba wajen samun masu tarin fuka a Najeriya.
Kalubalen tarin fuka a jihar Kano
Wata ma’aikaciyar lafiya mai suna, Jane Adizue ta bayyana cewa ana fuskantar kalubale da dama dangane da tarin fuka a Kano.
Jane Adizue ta ce akwai kalubalen rashin gwaji da wuri, rashin samun kulawa da rashin bayyana yadda mai cutar ya kamata ya rayu.