Yara 22,500 ne Suka Mutu a Legas Sakamakon Shaƙar Gurbatacciyar Iska  – LASEPA

Hukumar kula da muhalli ta Legas, LASEPA, ta ce yara aƙalla 22,500 ne suka mutu sakamakon shaƙar gurbatacciyar iska a 2021.

A wata sanarwa da ta fitar hukumar ta ce kashi 75 cikin mutum 30,000 da suka mutu a 2021 gurɓacewar iska ce sanadi.

Shugabar hukumar, Dr Dolapo Fasawe, ta ce sun samu wadannan alkaluma ne daga rahotanni da suka tattara kan tasirin sauyin yanayi ga lafiyar al’umma.

Dr Dolapo ta ce gwamnatin Babajide Sanwo-Olu na fadi tashin ganin yada zai inganta tsafta a birnin Legas da al’ummarta.

Ta umarci mutane su rage amfani da makamshi mai gurbata muhalli da amfani da fitilar zamani maimakon kalanzir da itace da gawaye.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here