Yara Biyu Sun Rasa Rayukan Su a Suleja Sakamakon Gobara
Allah ya yi wa wasu yara biyu rasuwa a Anguwar Dawaki da ke Suleja, Jahar Niger.
Hakan ya faru ne sakamakon gobara da ta tashi a gidansu a daren ranar Alhamis.
Alhassan Jibirin Yanji, mahaifin yaran ya yi kokarin ceto su amma hakan bai yi wu ba.
Yara biyu, Suraiya mai shekaru 7 da Habib mai shekaru 9 sun kone sakamakon wata gobara da ta kona wani babban gida a Anguwar Dawaki a garin Suleja da ke jahar Niger.
Daily Trust ta ruwaito cewa mahaifin yaran, Alhaji Jibrin Yanji, wanda ya samu rauni garin kokarin ceto yaran yana karban magani a asibiti da ke Suleja.
Read Also:
Wani mazaunin garin, Bashir Ibrahim, ya ce gobarar ta faru ne a daren ranar Alhamis misalin karfe 3 a lokacin da wuta ta kama a dakunan da wadanda abin ya shafa suke ciki.
Ya ce yaran suna kwance a dakinsu yayin da mahaifinsu yana dakinsa, a lokacin da ya farka sai ya lura hayaki ya turnuke gidan baki daya.
Ya ce, “Abin mamaki babu wutar lantarki a dukkan unguwar ta Dawaki a lokacin da gobarar ta tashi don haka babu wanda ya san sanadin gobarar.”
Daga bisani an yi wa yaran jana’iza bisa koyarwar addinin musulunci a safiyar Juma’a.
Ya bayyana cewa babu wani abin amfani da aka ciro daga gidan domin mahaifiyar yaran ma bata gida a lokacin da abin ya faru.
Shugaban karamar hukumar Suleja, Alhaji Abdullahi Maje, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce ana bincike domin gano sanadin gobarar.