Adadin Yara da ke Rayuwa Cikin Tsananin Talauci a Duniya – UNICEF

 

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya fitar da wani rahoto da ke cewa kimanin yara miliyan 333 na rayuwa cikin kangin talauci a duniya.

Rahoton na UNICEF da hadin gwiwar Bankin Duniya ya nuna cewa tsananin talaucin na da nasaba da annobar korona da sauran kalubale da dama da suka hada da sauyin yanayi.

Rahoton ya ce alkaluma sun nuna cewa yaro daya cikin shida na rayuwa a kan kasa da dala biyu a kowacce rana.

A cewar rahoton, nahiyar Afirka ta yamma da Sahara na cikin wuraren da ke da mafi yawan yara kanana da adadinsu ya kai kashi 40 cikin 100 wadanda ke rayuwa a wani mawuyacin hali na tsananin talauci.

Bayan wani bincike da aka gudanar shekaru goma da suka wuce, an gano cewa yankin Afirka ta yamma da sahara ya daga daga matakin da aka san shi, inda a shekarar a 2013 ya ke da kashi 54.8, a 2022 kuma ya koma kashi 71.1 cikin dari.

Akwai dai manyan dalilai da aka bayyana da ke taka rawa wajen karuwar talaucin da suka hada da karuwar jama’a cikin sauri da rikici da ta’adin annobar korona da sauyin yanayi mai nasaba da aukuwar itila’i daban-daban, wadanda sun taimaka wajen munana yanayin.

A cewar rahoton na UNICEF, yara da ke gidaje matalauta na fama da kalubalan rayuwa da suka danganci rashin wadataccen abinci da wurin kwana da ingantaccen kiwon lafiya da ilimi, wadanda abubuwa ne da za su taimake su a rayuwa.

Rahoton na UNICEF ya kara da cewa irin wadannan yaran na rayuwa ne a yankunan karkara da kuma wadanda ke zaune a gidaje matalauta inda galibin iyayensu na da karancin ko rashin ilimi.

Daga bisani UNICEF, ya zayyano wasu muhimman matakan da ya ce gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu a duniya su lura da su,ciki har da mayar da hankali wajen tallafawa yara da ke rayuwa a kasashen da ke fama da tsananin talauci ko a yankunan da ke fuskantar rikici.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com