Amurka ta Nada ‘Yar Najeriya a Matsayin Daraktar Harkokin Afrika

‘Yan Najeriya a fadin duniya na nuna bajintansu a bangarori daban-daban na rayuwa.

Wata mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Zainab Usman, ta samu mukami a Amurka.

Zainab Usman ta samu shiga Carnegie Endowment a matsayin daraktar harkokin Afrika.

Wata ‘yar Najeriya, Zainab Usman, ta ciri tuta a Amurka yayinda aka nada ta Daraktar harkokin Afrika a Carnegie Endowment.

An sanar da nadin Zainab ne ranar Talata, 2 ga Febrairu, 2021. Zainab ta yi karatun doktoranta a jami’ar Oxford dake Ingila.

Tsokaci kan sabon mukamin da ta samu a Tuwita, Zainab ta ce wannan shiri na harkokin Afrika zai bada gudunmuwa wajen bada shawarin tattalin arziki, siyasa, fasaha, da abubuwan da suka shafi Afrika.

Binciken da Legit.ng ta gudanar ya nuna cewa gabanin yanzu, Zainab ta yi aiki bankin duniya.

A bankin, tayi aiki kan cigaba tattalin arziki, tattalin ma’adinan kasa da kuma fasaha.

Ta yi aiki kan wadannan abubuwa a kasashe irinsu Cote d’Ivoire, Morocco, Nigeria, Papua New Guinea, the Republic of Congo, Serbia, Tanzania, da Uzbekistan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here