‘Yar Asalin Najeriya ta Zama Magajiyar Gari a Birtaniya

Pauline Akhere George, yar asalin karamar hukumar Esan ta Gabas a Jihar Edo ta zama Magajiyar Garin Lambeth Borough a Birtaniya.

Ms Akhere George ce mace ta farko, haifafiyar Najeriya da ta fara rike mukamin magajiyar garin Lambeth a tarihin kafuwar garin.

A yayin bikin rantsar da ita, sabuwar magajiyar garin ta mika godiya na musamman ga wadanda suka zabe ta da kuma yan uwanta a gida Najeriya.

Birtaniya – An zabi Pauline Akhere George, haifafiyar Najeriya kuma yar Birtaniya a matsayin magajiyar garin Lambeth Borough, Landan a Birtaniya na shekarar 2022/2023, rahoton Nigerian Tirbune.

Bayan zabenta, Ms George, yar asalin Okhuessan, daga karamar hukumar Esan ta Gabas a Jihar Edo ta zama mace na farko yar Najeriya da ta fara zama Magajiyar Lambeth Borough.

A wurin bikin rantsar da ita da aka yi a dakin taro na Lambeth, ta yi jinjina ga masu kada kuri’a da suka karrama ta suka zabe ta don yi musu hidima.

Jaridar ta Nigerian Tribune ta rahoto cewa tsohuwar mataimakiyar Magajiyar Garin na Lambeth na 2020/2021 ta kuma yi godiya ga yan uwanta da ke gida a Najeriya.

Mahaifiyar sabuwar magajiyar garin, gimbiya daga gidan sarauta na Alenkhe kwararren malamar jinya ne da ya yi karatu a South Columbia School of Nursing, England da Thames Valley University, England.

Ta kuma yi karatun digiri na biyu a bangaren aikin shari’a daga Jami’ar London Metropolitan.

Pauline ta dade tana ayyukan yi wa al’umma hidima a garin Lambeth Borough

Aunty Pauline, kamar yadda aka fi saninta, ta yi aiki a National Health Scheme (NHS) inda ta taimaki mutanen unguwarta lokacin COVID-19 kuma da wakilci malaman jinya a kotu a wurin aiki da kotun ma’aikata.

Ta kuma yi ayyuka da suka shafi yaki da laifuka na wuka da bindiga da samar wa matasa ayyukan yi da karfafa musu gwiwa su koyon makamashin aiki.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here