‘Yar Najeriya ta Kafa Tarihin Saka Karin Gashi da ya Kai Tsawon Mita 351.28
Wata ‘yar Najeriya ta kafa tarihin shiga kundin bajinta na Guinness saboda sanya ƙarin gashi mafi tsawo da aka saka da hannu.
Helen Williams ta saka karin gashi da ya kai tsawon mita 351.28.
Helen ta shafe tsawon kwana 11 tare da kashe naira miliyan biyu wajen saka karin gashin.
Ta kuma yi amfani da gashi har ɗauri 1,000 da gwangwanin man feshi 12 da dankon jona gashi 35 da kuma karfen rike gashi 6,250.
Read Also:
“Wannan bajinta, na ɗaya daga cikin abubuwa mafi fice da na taɓa yi a rayuwa. Har yanzu na kasa yarda da cewa ni ce na yi,” in ji ta.
Duk da kasancewarta mai saka karin gashi tsawon shekara takwas, ta ce ba abu ne mai sauki ba saka karin gashi mafi tsawo a duniya, inda ta ce ta rika “jin matukar gajiya” a lokacin da ta kwashe tana yi.
“Kawaye da dangina ne suka karfafa min gwiwa. Kuma ba na so na ba su kunya, don haka na mayar da hankali sosai. Ga shi yanzu, sakamakon haka, na saka karin gashi mafi tsawo da aka taɓa yi da hannu a duniya,” Helen ta ce.