Daga Ado Abdullahi
Haƙiƙa tsarin Democraɗiyya tsari ne da ya ke bayar da damar masu neman kama madafun iko su baza komarsu domin neman goyon baya daga masu jefa ƙuri’a gabanin fara zaɓe. Ƴan siyasa kan yi duk wata dabara ta nuna su mutanen kirki ne, su masu taimakon talakawa ne, su masu kishin ƙasa ne. Duk dai domin talaka mai jefa ƙuri’a ya yarda da amincewa da su a lokacin da aka buga gangar kampen na siyasa.
Ƴan siyasarmu kan shiga kwararo-kwararo domin yaɗa manufa , wasu kan bi mutane har cikin gidajensu , masallatai, majami’u, gidajen mata masu zaman kansu, tasoshin mota, wuraren hira da dai sauransu.
Akan ware maƙudan kuɗaɗe domin neman goyon baya kama daga raba babura, motoci, turamen atampa, yadin shadda, sabulu, shinkafa kai har da garin kwaki da kwalin ashana a wasu wuraren.
Irin waɗanan ƴan siyasa bayan sun sami damar shiga gidajen gwamnati kama daga ta tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sai ka ji “ɗif”, kamar an yi ruwa an ɗauke a bisa alheran da suke yi kafin zaɓe. Ba za su ƙara damuwa ko kula da buƙatun al’ummar da suka zaɓesu ba, domin sun san ba cancanta ta kai su muƙaman ba. A’a kuɗin kawai suka saka, suka sayi talaka mai kwaɗayi.
Daman sun tsunduma ƙasa a talauci ne domin samun sauƙin ribatar talakawa. Wata karin maganar Bature tana cewa; Idan kana son karenka ya yi maka biyayya, toh ka horar da shi yunwa da ƙishirwa.
Wajibin masu kaɗa ƙuri’a ne su sani duk wanda ya sayi ƙuri’arka, to ya riga ya saye ƴancin da ƙasa ta ba ka. Kuma ya hana maka damar kaɗa ƙuri’a ga wanda zai inganta rayuwarka da ta al’ummarka kenan.
Read Also:
Ƴan siyasa sun shirya tsaf ranar zaɓe domin sayen ƙuri’un ragwayen cikinmu, waɗanda ba su iya jure ɗan kuɗin da ba zai biya musu buƙatar yini ɗaya a rayuwrsu ba. A wulaƙance wasu za su sayar da ƙuri’arsu a ƴan kuɗin da basu wuce Naira 200 zuwa 1,000 ba, domin rashin sanin ƴancin kansu da al’ummarsu.
Akwai haɗarin gaske wajen karɓar kuɗin hannun ɗan siyasa domin ya juya ra’ayin mutum don ya zaɓi wani. Duk da dai wasu malamai suna bayar da fatawar a karɓi kuɗin hannunsu wai a zaɓi wanda mutum ya ga yafi masa.
Ni kam ina da ra’ayi akasin haka. Me yasa talaka ba zai yi ƙyamar kuɗin ba gaba ɗaya? Domin matuƙar ana ƙyamar kuɗaɗen nasu ba za su juya talaka yadda suka ga dama ba. Za kuma su ji tsoron wulaƙanta masu kaɗa ƙuri’ar wajen nuna za su sayesu da ƴan kuɗi kaɗan. Bahaushe dai ya ce bayan kwaɗayi akwai wulaƙanci.
Toh yanzu lokaci ya zo da talaka zai kashe rana ya bi layi a tantanceshi, ya dawo ya kaɗa ƙuri’a. Wasu masu ƙoƙari su sake kashe dare su tsaya a ƙidaya, su raka har sai an tabbatar da abin da suka zaɓa.
Abin tausayi sai bayan ƴan siyasa sun shige gidajen gwamnati, sai ya zama tsakaninsu da talaka sai daga nesa. Amma su da ƴaƴansu, matansu da makusantansu rayuwarsu ta canja. Makarantu sai na ƙasar waje, asibiti sai a turai. Shi kuwa Mallam talaka an bar shi da hamma.
Toh lallai talaka ya kamata ya faɗaku, ya sani shi mutum ne mai daraja ba hajar sayarwa ba. Bai kamata mutum mai mutunci ya zama yana da farashi ba.
The post Zaɓen 2019: Walaƙantaccen Talaka Shi Yake Da Farashi appeared first on Daily Nigerian Hausa.