Zaben Kananan Hukumomi : Mutane na Dariya na sha Kaye a Akwatina Amma Demokradiyya ce ta yi Aiki – El-Rufa’i

 

Gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce kayan da APC ta sha a akwatinsa ya nuna jam’iyyar bata yi magudi ba.

Gwamna El-Rufai ya kuma ce masu zargin cewa gwamnati ta tsara wani yaudara da na’urar zaben sun ji kunya.

El-Rufai ya ce sakamakon zaben ya kuma nuna cewa kan mutanen Kaduna ya hadu sun fara zaben cancanta da aiki ba wai jam’iyya ba.

Nasir El-Rufai, gwamnan jahar Kaduna ya ce nasarar da jam’iyyar PDP ta samu na lashe zabe akwatinsa ya nuna cewa APC bata yi maguɗi ba da na’urar zabe na zamani, rahoton The Cable.

A ranar 4 ga watan Satumba, hukumar zabe na jahar Kaduna, KADSIECOM, ta yi zabe ta hanyar amfani da na’urar mai amfani lankarki.

Kafin wannan lokacin, Jahar Kaduna ce ta farko da ta fara amfani da wannan sabon tsarin zaben na zamani a Nigeria.

Sai dai, jam’iyyar APC ta sha kaye a akwatin El-Rufai yayin zabukan kananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar a jahar.

Idan da mun yi magudi ba zan fadi a akwati na ba, El-Rufai

Da ya ke magana a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin din Channels a ranar Litinin, El-Rufai ya ce sakamakon zaben ya nuna cewa jam’iyyar mai mulki ba ta yi magudi ba wurin tsara na’urar zabukan kamar yadda The Cable ta rawaito.

Ya kuma ce sakamakon ya nuna babu rabuwan kai a jahar sannan, ya kara da cewa hakan hujja ne da ke nuna mutane sun fara yin zabe bisa aikin da wadanda suka zaba suka yi.

Ya ce:

“Wadanda suka kai rahoto cewa an sauya tsarin na’urar don yin magudi zun ji kunya a lokacin da aka ruwaito cewa APC ta sha kaye a akwati na. Mutane na dariya cewa na sha kaye a akwati na amma demokradiyya ce ta yi aiki.”

“Ba suna na bane a takardan zaben don haka ba hujja bane a kai na, hukka ne kan kansilar da shugaban karamar hukuma.

Rashin nasara a akwatin zabe na ya nuna cewa ba mu yi magudi ba ko lalata na’urar, ba mu yi wa hukumar zabe mai zaman kanta na jahar mu katsalandan ba kuma komai ya tafi dai-dai.

“Sakamakon zaben kawo yanzu ya nuna kan mutanen mu ya hadu dama shine abin da muke aiki a kai. Muna son mu canja yadda wasu ke dauka cewa jam’iyyar PDP na wani bangare ne a jahar, wani sashin kuma na APC. Wasu na cewa PDP na da alaka da wani addini, APC ma na da alaka da wani addini.

“Sakamakon zaben ya nuna cewa daga karshe dai mun hada kan mutanen Kaduna kuma mutane zuwa zabe bisa cancanta da aikin da wadanda suka zaba suka yi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here