Zaben Kananan Hukumomi: Lissafin APC na Neman Canza wa a Garin Ifako/Ijaye Dake Legas

 

Neman shugabanci ya raba kan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a garin Ifako/Ijaye.

Da farko ‘yan APC suna tare da Kofoworola Ajayi, yanzu lissafin ya canza.

Ana rade-radin masu ruwa da tsaki sun dawo goyon-bayan Deacon Omole.

Lagos – Rahotanni daga jaridar Punch sun bayyana cewa ana fama da rikicin gida a jam’iyyar APC a yankin karamar hukumar Ifako/Ijaye a jahar Legas.

An samu sabani tsakanin mabiya jam’iyyar ta APC ne a sakamakon zaben shugabannin kananan hukumomi da aka gudanar a makon da ya gabata.

Jaridar tace hanyar da za a bi wajen tsaida shugabannin jam’iyyar APC a matakin kananan hukumomi ne ya raba kan wasu daga cikin ‘yan APC.

An yi wa Kofoworola Ajayi mubaya’a

Wata takarda da ta shiga hannun ‘yan jarida ta nuna masu ta-cewa sun tsaida Kofoworola Ajayi a matsayin wanda za ta zama shugabar APC a Ifako/Ijaye.

Shugabannin APC da jagororin jam’iyyar mai mulki a Ifako/Ijaye sun amince da Kofoworola Ajayi. Amma abubuwa suna neman canza zani a halin yanzu.

Daga cikin wadanda suka yi mata mubaya’a akwai; Otunba Yomi Ogunnusi; Nurudeen Akinwunmi, Toba Oke, Dayo Fafunmi, da Akin Fadayomi.

Sai Salvador Adebayo, Rotimi Adeleye, Temitope Adewale, Demola Doherty, Usman Hamzat, Seni Tobun, Kunle Olayinka, Rajh-Label, da kuma Banjo Omole.

Lissafi yana neman ya canza

Daga baya sai aka ji ana cewa irinsu Temitope Adewale sun ziyarci Bola Tinubu a Landan, inda aka canza yadda za a fito da shugabannin jam’iyyar APC.

“Bayan duk mun yarda da sunayen da aka fitar, wasu sun canza ra’ayi. Suna ikirarin Tinubu bai gamsu da matakin ba, suka kira shi a waya, suka kai kuka.”

“Muna kira ga Tinubu ya yi magana a kan murde zaben da ake shirin yi. Wannan ne abin da ya faru a lokacin zaben shugabannin kananan hukumomi.”

Majiyar tace bayan an tsaida magana daya a kan Ajayi, yanzu an fara neman yadda za a ba Deacon Omole wannan kujera, akasin yarjejeniyar da aka yi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here