Zaftarewar ƙasa ta yi Ajalin Mutane 158, da Dama Sun ɓace a Indiya

 

 

Adadin mutanen da suka mutu sanadin ibtila’in zaftarewar ƙasar da ta afku a jihar Kerala da ke kudancin Indiya sun kai 158, sai wasu 187 da jami’ai suka ce ba a san inda suke ba.

An dawo aikin ceton da aka dakatar cikin daren Talata.

Zaftarewar ƙasar ita ce bala’i mafi muni da ya afku a jihar tun 2018 lokacin da ambaliyar ruwa ta yi ajalin fiye da mutum 400.

An yi ƙasa-ƙasa da tutar ƙasar a gine-ginen gwamnati yayin da ake makokin kwanaki biyu a faɗin jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here