Zaki ya Tsere a Afirka ta Kudu ya Shiga Gari

 

Rundunar ‘yan sandan Afrika ta Kudu ta gargaɗi al’ummar wani yanki bayan da wani zaki ya tsere daga cikin wata mota da ake tafiya da ita a lardin Arewa maso Yammacin Ƙasar.

An ce zakin ta tsere ne a lokacin da mai ita ya ɗauke ta a bayan wata babbar mota.

Ba a bayyana ainihin lokaci ko yadda zakin ya tsere daga cikin motar ba, inda sai da mai ita ya isa inda zai je a garin Tlakgameng sannan ya gane ta tsere, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

A yanzu ma’aikatan gandun daji da manoma na aikin farautar zakin.

Rundunar ‘yan sandan ta bukaci duk wanda ya ga zakin da ya kai rahoto ga hukumomin kula da muhalli.

Hakan na zuwa ne bayan da wasu damisa biyu suka tsere a watan da ya gabata a lardin Gauteng.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here