Zakuna Sun Afkawa ‘Yan Ta’adda a Mozambique

 

Jami’an tsaro a kasar Mozambique sun bayyana yadda zakuna suka yi kalace da wasu ‘yan ta da kayar baya.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an samu wata kungiyar ‘yan ta’adda da ke kangarar da jama’a bayan jawo su cikinsu.

An yawan samun kungiyoyin ta’addanci da ke tasowa a nahiyar Afrika, lamarin da ke kara sanya tsoron a zukatan jama’a.

Mozambique – Rundunar sojin Mozambique ta ce ta kama wasu tsageru da ke alanta jihadi a yankin kasar, inda suke horar da jama’a kan akidarsu kana wasu 16 sun mutu.

Rahoton BBC Hausa ya ce, mutum hudu aka kama da zargin kafa kungiya haramtacciya tare da yaudarar mutane suna shiga gami da daura su a mummunar hanya.

Bernardino Rafael, kwamandan ‘yan sanda a kasar ne ya bayya hakan, inda yace mutane 16 da suka mutu sun mutu ne sakadamakon arangama da sojoji.

A wani yanayi mai ban mamaki, ya kuma ce zakuna da kadajoji ne suka afka ma wasu daga cikin ‘yan ta’adda.

Rafael ya bayyana wadannan maganganu na kamu da hallaka ‘yan ta’adda ne a yayin ganawa da mazauna yankin Quissanga a Cabo Delgado ta Arewacin Mozambique.

Sai dai, rahoton ya ce Rafael bai fadi adadin ‘yan ta’addan da dabbobin suka kashe ba, duk da tabbacin da ya bayar na gudunmawar dabbobin a hallaka tsagerun.

Kwamandan ya ce hukumomi za su yi kokarin binne tsagerun da ake da gawarwakinsu a hannu, kamar yadda jaridar CNR ta ruwaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here