Bayan Fitowarsa Daga Kurkuku: Zakzaky ya Magantu Kan Masu Son Wargaza Kungiyarsa

 

Shugaban IMN, Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya gana da wakilan kungiyarsa da wasu kungiyoyi a Abuja.

Karon farko bayan fitowarsa daga kurkuku, Zakzaky yace duk kokarin tarwatsa tafiyar shi’a ba zai samu nasara ba.

Malamin ya kuma yi ta’aziyya ga mabiyansa bisa lamarin da ya faru tsakaninsu da sojoji a 2015.

Abuja – Shugaban kungiyar mabiya akidar shi’a (IMN), Sheikh IbrahIm El-Zakzaky, ranar Talata yace duk mai son wargaza tafiyarsa ba zai ci nasara ba.

Zakzaky yayi wannan maganar ne a taronsa na farko da wakilan kungiyarsa na jihohi da wasu kungiyoyi a Abuja, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Malamin yace duk wata bita da kulli da akewa kungiyar IMN, wanda ya jawo aka tsare shi tsawon shekara 6, ba abinda zai kara wa kungiyar sai farin jini a idon duniya.

Mun fuskanci kalubale a 2015

Sheikh Zakzaky yace:

“Ko da makiya sun ɗaura ɗamarar yakar mu, ba zasu sami nasara ba illa su kara ɗaukaka kungiyar mu zuwa wani matsayi da bamu yi tsammani ba.”

“Lokacin da aka karkashe mu a Zaria a shekarar 2015 yana da wahalar jurewa domin ya shafi mutane da dama.”

Ya yabawa kungiyoyi da suka taimaka

Shehin malamin ya nuna jin daɗinsa ga kungiyoyin kare haƙkin ɗan adam na gida da waje bisa jajircewarsu wajen ganin an sake shi.

Hakanan ya gode wa mabiyansa waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu, da waɗanda suka ji rauni duk dominsa, kamar yadda sahara reporters ta ruwaito.

Shugaban yan shi’a ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa yan uwansu da masoyansu yayin rikici da sojoji a Husainiyya.

Ya kuma yi addu’an Allah ya jikansu da rahama yasa aljannar ta zama ita ce makomarsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here