Ya Kamata mu Zama Masu Gaskiya Dangane da Albarkatun da Allah ya ba mu – Remi Tinubu

 

Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su tashi don ƙara shiga harkar noma, inda ta ce ƙasar za ta iya samarwa kanta isasshen abinci.

Remi ta faɗi haka ne a lokacin da ta karɓi bakuncin mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina Mohammed a ofishinta ranar Laraba a fadar gwamnati da ke Abuja.

Uwargidan shugaban ƙasar ta bayyana cewa, ɓullo da shirye-shirye daban-daban da gidauniyarta ta Renewed Hope Initiative ta yi, musamman a fannin noma, samar da aikin yi, ilimi, lafiya da jin daɗin jama’a, duka ta yi shi ne don ƙara karfafa irin ƙoƙari da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke yi.

“Shugaban ƙasa ya ɗauki matakan da suka dace. Waɗannan matakai za su taimaka mana wajen gina Najeriya. Ya kamata mu zama masu gaskiya dangane da albarkatun da Allah ya ba mu,” in ji Remi.

Ta kuma nanata buƙatar zaburar da matasa wajen yin tunanin da ya dace a kan ƙasar.

Dangane da batun ‘yan gudun hijira, Sanata Tinubu ta ce gidauniyarta ta fara shirin ciyar da ‘yan gudun hijira da nakasassu abinci duk wata.

Ta ce ba za ta gajiya ba, za ta ci gaba da yi wa ƴan Najeriya duk abin da za ta iya.

A jawabinta, mataimakiyar Sakatare Janar na MDD, Aisha Mohammed, ta bayyana cewa Majalisar na yin wani shiri don tallafawa matasa, mata da kuma ƴan mata a Najeriya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here