Rashin Tsaro: Gwamnatin Zamfara ta Garƙame ƙananan Hukumomi Uku

 

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta ɗauki matakin dakatar da kowace irin hada-hada a wasu yankunanta da ke fama da matsalar tsaro.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a yau Juma’a, ta ce ta lura da yadda ake samun taɓarɓarewar tsaro ta hanyar sace-sacen al’umma a kauyuka da kuma kan wasu hanyoyin jihar.

A saboda haka sanarwar ta ce gwamnati ta kulle, ɗungurungum, ƙananan hukumomin Anka da Bukuyum da kuma Gummi.

Sauran kauyukan da kullewar ta shafa su ne Ƴarkofoji, da Birnin Tudu, da Rini, da Gora Namaye, da Janbako, da Faru, da Boko da kuma Mada.

Sanarwar ta kuma ce daga yau an rufe kasuwannin Danjibga da Bagega.

Bugu da ƙari an dakatar da zirga-zirga kan hanyoyi kamar haka:

– Colony zuwa Lambar Boko

– Bakura zuwa Lambar Damri

– Mayanchi zuwa Daki Takwas zuwa Gummi

– Daki Takwas zuwa Zuru

– Kucheri zuwa Bawaganga zuwa Wanke

– Magami zuwa Dangulbi

– Gusau zuwa Magami

Gwamnati ta ce an ɗauki matakin ne domin bai wa jami’an tsaro damar gudanar da ayyukansu ba tare da wani cikas ba.

Ta kuma ce ta bai wa jami’an tsaro umurnin ɗaukan mummunan mataki kan duk wanda aka samu da laifin karya dokar.

Zamfara na cikin jihohin da matsalar tsaro ta ƴanfashin daji ta fi tagayyarawa a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here