Masu Ruwa da Tsaki a Jihar Zamfara na Goyan Bayan Tinubu Saboda Gaskiyarsa, Adalci da Rikon Amana – Sanata Kabiru Marafa
Takarar Asiwaju Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ta samu tagomashi daga arewacin Najeriya.
A yayin da babban zaben shekarar 2023 ke karatowa, mutanen Zamfara sun sake goyon bayan takarar Tinubu yayin da suke cewa yana da gaskiya da amana tsakanin yan takarar.
Sanata Kabiru Marafa, jagoran kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC ga gwamnan jihar za su cigaba da yi wa Tinubu kamfen gabanin zaben 2023.
Zamfara – Shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, PCC, a Zamfara ya ce masu ruwa da tsaki a jihar suna goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu saboda gaskiyarsa da adalci da rikon amana.
Ya bayyana hakan ne cikin sanarwa da ya fitar a Gusau a ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba ta bakin sakataren watsa labarai na APC, Malam Yusfu Idris, Vanguard ta rahoto.
Jigon APC ya yi magana kan dalilin da yasa Arewa ke goyon bayan Tinubu
Read Also:
Marafa, a wurin taron da kungiyoyin unguwanni, ya yi magana kan bukatar cigaba da tattaunawa kan cancanta da iya aiki na dan takarar na APC, The Nation ta kara.
Idris ya ce:
“Shugabannin PCC na Zamfara karkashin jagirancin Sanata Marafa, na cigaba da tattaro wa Sanata Tinubu magoya baya da Gwamna Matawalle, da yan takarar APC a babban zaben 2023.
“Shugabannin unguwanni da dama sun halarci taron da ka yi a gidan gwamnatin jihar Zamfara da ke Gusau.”
Marafa ya aika sako ga shugabannin jam;iyyar APC a yan Najeriya
A cewar sanarwar, Marafa ya yi kira ga shugabannin unguwanni su goyi bayan Tinubu saboda adalcinsa, gaskiya, amintaka da rikon amana, yana mai cewa shi mutum ne mai tsoron Allah.
Sanarwar ta kara da cewa:
“Ya nemi goyon bayansu don hada kan masu zabe, musamman a wuraren taruwa, don su zabi yan takarar APC.
“A matsayinku na shugabanni da ke kusa da mutane, ana matukar girmama kuma galibi mutanen ku na jin maganan ku.
“Takarar Tinubu da Shettima zai kawo cigaba mai dorewa, daga tattalin arziki, inganta tsaro, samar da arziki tsakanin mutanen.”
Marafa ya yi kira ga mutanen su yi addu’ar dawowar zaman lafiya a jihar.
A Dalilin Da Yasa Arewa Take Goyon Bayan Tinubu, Sanata Mai Karfin Fada A Ji A APC Ya Yi Magana, Ya Fada Dalili Mai Muhimmanci.