Gwamnan Jahar Zamfara ya Koka da Rashin Tsaro a Jaharsa
Gwamnan jahar Zamfara ya bayyana halin da jaharsa ke ciki na yawaitar aikata muggan laifuka.
Gwamnan ya koka kan ta’azzara da ta’addanci ke yi a fadin jahar cikin makwannin da suka gabata.
Ya bukaci jama’ar jaharsa da su kare kansu daga ‘yan ta’adda duk lokacin da aka kai musu hari.
Bello Matawalle, gwamnan jahar Zamfara, ya ce kalubalen rashin tsaro a jahar na kara ta’azzara, TheCable ta ruwaito.
A wani furuci na gwamnan a ranar Asabar, Matawalle ya ce ‘yan ta’adda sun koma yadda suke a da kafin zuwan gwamnatinsa.
duk da kokarinta na rage yawaitar ta’addanci. Ya koka kan yadda lamurran ta’addanci ke ci gaba da ta’azzara tare da bayyana yadda rashin tausayin ‘yan ta’addan ke damunsa.
Read Also:
A kalamansa, gwamna ya ce: “A cikin makonnin da suka gabata, aikita ta’addanci ya sake komawa kamar yadda yake a da kafin zuwan gwamnatina.”
“Mahara suna kashe mutane ba tare da la’akari da hankali ba. Mata, tsofaffi, da yara ba su tsira ba.
“A sakamakon haka, mutane da dama sun rasa muhallansu a kusan kowane gari a jahar. “Ku shaidu ne a kan abin da muka cimma tun daga farkon gwamnatinmu, musamman kokarin samar da zaman lafiya da sulhu da muka fara kuma muka cimma.
Gwamnan ya kuma bukaci al’ummomi su kare kansu daga ‘yan ta’adda yayin da ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da tsaro a jahar, in ji Channels Tv.
Yace:
“Ina tabbatar muku da cewa za mu ci gaba da jajircewa a kokarin da muke yi na kawar da ta’addanci da dukkan nau’ikan aikata laifuka daga Jaha.”
“A wannan yakin, babu wani da zai tsira. Duk wanda ke da hannu cikin wadannan ayyukan barna, komai girman matsayinsa, za a yi masa hukunci daidai da doka.”