Gwamnatin Zamfara ta Magantu Kan Zargin Biyan ‘Yan Ta’adda Kudin Sulhu

 

Jihar Zamfara – Gwamnatin jihar Zamfara ta nesanta kanta da sanarwar da aka ce ta fito daga gare ta na shirin tattaunawa da yan ta’adda domin sulhu.

Sakataren gwamnatin Zamfara, Malam Abubakar Nakwada ne ya musanta takardar yayin tattaunawa da manema labarai a Gusau.

Radio Nigeria Kaduna ta wallafa Malam Nakwada na cewa takardar da ake cewa ta fito daga ofishinsa na fara shirin ganawa da jagororin yan ta’adda a jihar ta bogi ce.

Gwamnati ta kafe kan kin tattaunawa da yan ta’adda

Jaridar Solace Base ta wallafa cewa gwamnatin Zamfara ta kafe kan matsayarta na kin tattaunawa da yan ta’adda da su ka addabi jihar.

Sakataren gwamnatin jihar, Malam Abubakar Nakwada ya ce a wannan matsayar suka fara mulki, kuma har yanzu su na kan wannan.

Zamfara: Gwamnati, yan sanda sun dauki mataki

Malam Nakwada ya ce gwamnatinsu ta yi takaicin labarin da ke cewa ta biya wasu masu yada labarai a kafafen sada zumunta domin fito da labarin sulhu da yan ta’adda.

Sakataren gwamnatin ya ce babu kamshin gaskiya a labarin, kuma yanzu haka yan sanda suna kan batun domin zakulo wadanda suka fitar da takardar bogin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here