Gwamnatin Zamfara ta Nada Sabon Shugaban Ma’aikatan Jahar

 

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya amince da nadin Alhaji Kabiru Muhammad Gayari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan jahar.

Hadimin gwamnan, Yusuf Idris Gusau ne ya tabbatar da nadin a yau Talata, 24 ga watan Agusta.

Nadin ya biyo bayan daukaka tsohon shugaban ma’aikata zuwa sakataren gwamnatin jahar.

Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jahar Zamfara ya amince da nadin Alhaji Kabiru Gayari a matsayin sabon shugaban ma’aikata na jahar, jaridar The Nation ta rawaito.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da darakta janar na yada labarai da wayar da kan jama’a da sadarwa na jahar, Alhaji Yusuf Idris ya fitar a Gusau ranar Talata, 24 ga watan Agusta.

Nadin ya biyo bayan daukaka tsohon shugaban ma’aikata, Alhaji Kabiru Balarabe zuwa sakataren gwamnatin jahar (SSG), jaridar Daily Post ta rawaito.

A cewar sanarwar, nadin Kabiru Muhammad Gayari a matsayin Shugaban Ma’aikata ya fara aiki nan take.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ba da rahoton cewa Gayari, ya kasance Babban Sakatare na Ma’aikatar Kudi har zuwa lokacin da aka nada shi.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here