Akwai Yiyuwar Gwamnatin Zamfara ta Kara Rufe Hanyoyin Sadarwa na Zamani a Karo na Biyu
Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce za ta iya sake rufe hanyoyin sadarwa na zamani a jihar idan bukatar hakan ta sake tasowa.
Zailani Bappa, hadimin Gwamna Bello Matawalle ne ya yi wannan karin bayanin yana mai cewa amma a yanzu gwamnan bai bada umurin a rufe hanyoyin sadarwan ba.
Gwamnatin na Jihar Zamfara ta jajantawa iyalan mutanen da yan bindiga suka sace a baya-bayan nan a Bebeji Plaza ta kuma ce tana aiki da hukumomin tsaro da aiwatar da wasu sabbin tsare-tsare.
Jihar Zamfara – Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa akwai yiwuwar ta sake katse hanyoyin sadarwa na zamani a jihar karo na biyu idan bukatar hakan ya taso.
Mashawarcin Gwamna Matawalle na musamman kan kafafen watsa labarai, Zailani Bappa, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce gwamnatin ba ta riga ta datse hanyoyin sadarwar ba kamar yadda ake yadda jita-jita, rahoton The Punch.
Read Also:
Amma, ya ce, ‘Idan bukatar datse hanyoyin sadarwar ya taso, ana iya sake datse hanyoyin sadarwar.’
Bappa ya jadada cewa ya zama dole ya yi karin haske kan wasu labarai marasa tushe da aka ce sun fito daga ofishinsa game da rufe hanyoyin sadarwar a jihar.
Kalamansa”
“Mai Girma, Dr Bello Mohammed Matawalle, ya nuna damuwarsa bisa hare-haren yan bindiga a jihar, da kulawa da wadanda abin ya shafa ya kuma jajantawa iyalan wadanda aka sace a Bebeji Plaza a baya-bayan nan.
“Ba jajantawa kawai gwamnati za ta yi ba kaman kowa, amma ta sanar da al’umma matakan da ta dauka don magance kallubalen.
“Don haka, Mai Girma gwamna ya bayyana matsayin gwamnati a wannan lokacin.
“Mai girma ya ce ya tuntubi dukkan hukumomin tsaro a jihar don bullo da sabon tsari don magance kallubalen da yan bindigan, musamman yanzu da damina ya zo, wanda zai bada daman a aiwatar da sabbin matakan.
“Ya kuma ce idan bukatar rufe hanyoyin sadarwa ta taso, za a sake iya yin hakan.
“Amma mai girma gwamna bai sanar da rufe hanyoyin sadarwa ba, kuma bai umurci hukumomin su aiwatar haka ba.
“Wannan shine gaskiyar abin da ya faru.”