Daga Mahmud Isa Yola
Masu ta’addanci, da masu taimakawa ‘yan ta’adda, da shugabannin da suke sakaci har ta’addanci yayi tasiri akan al’umman su suna samun kwarin guiwa ne daga abubuwa guda hudu: rashin sanin illan abunda suke yi, sanin abunda suke yi amma ba tare da kulawa da musibar da zai janyo ba, sanin illan abunda suke yi yayin da suke tunanin cewa zasu iya kaucewa musiban idan ya tashi shafan su, ko kuma kin yadda cewa abunda suke yi yana da illa.
Ba sabon labari bane a wurin mu cewa jihar Zamfara a Nijeriya ta zama cibiyar aiwatar da ta’addanci ta yanda yanzu ana lissafin kusan kowani rana ana asaran rai a Zamfara ko kuma ayi garkuwa da masu rai. Ta’ddancin kashe-kashen ba ya tsaya akan wani sashi na al’umma day aba, ana kamawa kuma a kashe matasa, ana kamawa, kashewa ko fyade ga mata, ana kamawa ko kashe tsofoffi, kai hatta kanan yara ba’a barsu cikin wannan fitinar ba.
Idan mukayi nazarin tarihin ta’addanci a Zamfara zamu fahimci cewa wannan ba shine karo na farko da fitinan ke addaban jihar ba. Asali ma, lokacin da dan takaran shugaban kasa Muhammadu Buhari yake yakin neman zaben 2015, gwamna Abdul’aziz Yari yayi alkawarin cewa ta’addancin zai zo karshe idan mutane suka bashi hadinkai wajen zaben Muhammadu Buhari.
An zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari sama da kowani dan takara a jihar Zamfara, kuri’ar da shugaba Buhari ya samu a Zamfara ko Abdul’aziz Yari, gwamnan jihar bai samu ba. Yanzu muna neman shekaru hudu kenan karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari, amma ta’addanci da sace mutane a Zamfara bai tsaya ba, asali ma, a karkashin shugaba Buhari ne aka samu kashe kashe-kashe da sace-sace irin wanda jihar Zamfara bata taba samu ba. Ba wani Buhari muke magana ba, muna magana akan mai bada umurni na kololuwa ga dukkan jami’an tsaro Nijeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Tarihi zai hukunta shugaban kasa Buhari, cewa a karkashin mulkin sa ne aka samu wannan ta’addanci irin wanda jihar Zamfara bata taba gani ba. Marayu baza su ta ba mantawa da cewa an kashe iyayen su ne a karkashin mulkin sa ba, mata da suka rasa mazajen su baza su taba mantawa da cewa karkashin shugabancin Buhari aka kashe mazajen su ba, iyalai da ‘yan uwan wadanda akayi garkuwa da su, magidanta da aka kone gidajen su, fasinjoji da aka tare aka kashe a kan hanya… duka wadannan idan wani zai manta to tarihi bazai manta ba. wannan bakin fanti ne da bazai sharu ba a jikin shugaba Buhari.
Tabbas ba shugaba Buhari kadai ba, gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari, shugaban rundunar ‘yan sanda na kasa Ibrahim Idris da dukkan wadanda Allah ya dorawa alhakin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jihar Zamfara tarihi bazai manta da abunda ya faru karkashin kulawar ku ba.
Read Also:
Duk wanda yake rike da mukami, matukar yana da kuzarin amsawa idan an ambaci mukamin sa, to ya sani, ko yana so ko baya so shine yake da alhakin wannan mukami. Idan wani abu ya faru, to babu wanda za’a kalubalanta sama da shi. Kuma ya tanadi hujjan da zai baiwa Ubangijin sa.
Ta kowani bangare akwai matsaloli. Bincike na ya nuna min cewa ba shugabanni ne kadai sukayi sakaci ba. Yanzu haka gwamnatin jihar Zamfara na kokarin gurfanar da masu rike da mukaman gargajiya na yankunan da ake gudanar da ta’addanci guda bakwai a gaban kotu, bayan an tube su daga sarauta bisa zargin su da hannu a ta’addanci. Wannan yana nuna mana ba kawai shugabannin hukumomi ba, shugabanni mafi kusa da talaka (masarautun gargajiya) suma sun taka rawar gani a tasirin ta’addanci a jihar Zamfara.
Jaridar Punch ta ranar 17/02/2018 ta ruwaito gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari yana cewa sun sunar da jami’an tsaro akwai yunkurin da ‘yan ta’adda suke yi na kai hari a wani kauye. Yari yace sun sanar da jami’an tsaro awa 24 kafin ‘yan ta’addan su kawo harin, amma hakan bai saka jami’an tsaro daukan matakin dakile wannan harin ba. ikon Allah!
Mai martaba sarkin Zurmi shima a wannan rahoton an ruwaito shi yana cewa sun san inda ‘yan ta’addan suke fakewa inda nanne dukkanin su suke zama. Ya ambaci kauyen Kagara dake iyaka da Bafarawa na jihar Sokoto, kilomita kadan daga Shinkafi na jihar Zamfara. Wannan yana nuna kenan dukkan abunda ya kamata na hadinkai gwamnan jihar da Sarkin Zurmi sun bayar ga jami’an tsaro na samar da bayanai masu inganci.
Wannan rahoto anyi shi ne tun watan biyu, yau muna watan goma sha biyu. Watanni goma bayan da aka bayyana wa jami’an tsaro inda ‘yan ta’adda suke, amma abun mamaki, shekaran jiya a jihar Zamfara sai da ‘yan ta’addan nan suka kawo hari yanda suka saba.
Menene jami’an tsaro suke yi? Idan har akwai abunda suke yi, to na kusa da su su gaya musu cewa sun gaza a wurin gudanar da aikin su saboda ana kashe rayuka kullum a jihar Zamfara.
Wannan yasa daukan matakin gaggawa ya wajaba akan shugaban kasa Muhammadu Buhari da duk wani wanda ke da alhakin shugabantan wadanda ake kashewa. Idan har jami’an ‘yan sanda sun gagara, to ayi gaggawan sake tura sojoji wadannan wurare. Idan kuma kayan aiki ne babu to ayi gaggawan wadata su da kayan aiki, saboda ‘yan ta’addan nan bayanai sun nuna suna da makamai masu karfi. Jami’an tsaro su shiga wadannan kauyuka da dajin da ‘yan ta’addan suke samun mafaka su tarwatsa su. A tabbatar an ga bayan su gabadaya. Talakawa su bada hadinkai ta hanyar samar da isassun bayanai ga jami’an tsaro kuma gwamnati ta tsaya wajen tabbatar da an hukunta wadanda suke da hannu a wannan ta’addancin.
Allah ya bamu lafiya da zama lafiya a kasar mu Nijeriya, Amin.
The post Zamfara: Tarihi Zai Hukunta Shugaba Buhari appeared first on Daily Nigerian Hausa.