Zan Rufe duk Bankin da ya ƙi Karɓar Tsofaffin Takardun Kuɗi – Gwamnan Anambra
Gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya Charles Soludo ya umarci mazauna jihar da su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun naira 200 da 500 da 1,000 tare da sababbin takardun kuɗin a ko’ina cikin jihar.
Cikin wata sanarwa ta musamman da Charles Soludo – wanda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ne – ya fitar, ya ce babban bankin ƙasar ya umarci bankunan kasuwanci a ƙasar da su ci gaba da biyan masu ajiyar kuɗi a bankunan da tsofaffin takardun kuɗi.
Sannan kuma su ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin a duk lokacin da aka gabatar da su.
Read Also:
Gwamnan jihar ta Anambra ya ce ya tabbatar da sahihancin umarnin yayin wata hira da yayi da gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ta wayar tarho a ranar lahadi da daddare.
Soludo ya ce gwamnan CBN ya bayar da wannan umarnin ne yayin wani taro da babban bankin ya yi da bankunan ƙasar da aka yi a ranar Lahadi 12 ga watan Maris.
Gwamnan na Anambra ya kuma buƙaci al’ummar jihar da su kai ƙarar dukkan bankin da ya ƙi bin umarnin babban bankin na biya da karɓar tsofaffin takardun kuɗin.
Yana gargaɗin cewa gwamnatinsa za ta rufe duk bankin da ya bijire wa wannan umarnin.
A ranar 3 ga watan Maris ne kotun ƙolin Najeriya ya yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.
Wasu jihohin kasar ne dai suka shigar da ƙara a gaban kotun, suna neman a ɗage wa’adin da CBN ya sanya na daina amfani tsofaffin kuɗin.