Yadda Zanga-Zanga ta Kasance a Babban Birnin Tarayya
Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zanga domin tarwatsa su a Abuja, Babban birnin Najeriya.
Masu zanga-zanga an Abuja, babban birnin Najeriya sun mamaye titunan birnin suna bayyana takaicinsu ga tabarbarewar al’amura da matsalar yunwa a kasar.
Wata kotu a hukuncin da ta yanke ranar Laraba da daddare ta umarci masu zanga-zangar da su yi gangaminsu a filin wasa na kasa da ke wajen babban birnin a maimakon mamaye dandalin Eagle Square da ke tsakiyar birnin.
Sai dai bayan da suka yi dandazo a kofar shiga filin wasan ne masu zanga-zangar suka fasa shiga filin Hasan inda suka bar harabar wajen suka nufi cikin gari.
Read Also:
Zuwa yanzu babu cunkoson ababen hawa a birnin saboda wuraren kasuwanci har da bankuna na rufe. An jibge jami’an tsaro a muhimman wurare a Abuja.
Ana fargabar zanga-zangar na iya rikidewa zuwa tashin hankali saboda burus da umarnin kotu.
Wasu masu zanga-zangar da suka yi magana da BBC sun ce suna gudanar da zanga-zanga kamar yadda doka ta basu dama.
“Babban muradinmu shi ne a maido da tallafin mai. Ya kamata gwamnati ta janye da matakin da ta dauka,” in ji Abiodun Sanusi.
Suna kuma so gwmanati ta yi gagarumin garambawul a tsarin zaben kasar da bangaren shari’a.
“Abin da muke so shi ne kasar nan ta koma tsarin majalisa daya. A seke majalisar dattijai, a kyale majalisar wakilai,” Abiodiun ya bayyana.