Rashin Tsaro: An Gudunar da Zanga-Zangar Lumana a Jihar Filato

 

Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya, reshen jihar Filato ta gudanar da wani tattaki domin nuna adawa da matsalar tsaro da ke addabar jihar da ma wasu sassan yankin arewa ta tsakiyar Najeriya.

Tattakin ya gudana ne makonni kadan bayan munanan hare-haren da aka kai a wasu ƙauyukan jihar, waɗanda suka yi sanadiyyar aƙalla rayuka 100.

Waɗanda suka yi tattakin sun haɗa da maza da mata da matasa har da tsofaffi ɗauke da alluna wadanda aka rubuta wa saƙonni daban-daban.

A tattaunawarsa da BBC, Rabaran Gidion Para, wanda shi ne sakataren gamayyar majami’un jihar Filato ya ce maƙusudin tattakin shi ne domin kira ga gwamnati ta ɗauki mataki kan kashe-kashen da ake yi a yankin.

Jihar Filato da wasu jihohin arewa maso tsakiyar Najeriya na ci gaba da fama da matsalar tsaro duk da matakan da hukumomi ke cewa suna ɗauka domin kawar da matsalar.

Rikici tsakanin manoma da makiyaya da kuma rikice-rikice masu alaƙa da bambancin addini da na ƙabila sun haifar da rasa rayukan ɗaruruwan mutane da tarwatsa wasu daga matsugunansu.

A makon da ya gabata gwamnan jihar Filaton, Caleb Manasseh Mutfwang ya sanar da ɗaukan wasu sabbin matakai na daƙile matsalar, ciki har da hana kiwon dare da kuma farfaɗo da ƙungiyoyin ƴan sintiri na sa-kai.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here