Tsohon Jigon IPOB ya Zargi Kungiyar da Kashe Dr Chike Akunyili

Wani tsohon jigo a haramtacciyar kungiyar IPOB ya bayyana IPOB a matsayin ‘yan ta’adda.

Ya bayyana cewa, ‘yan IPOB ne suka kashe mijin marigayiya tsohuwar minista Dora Akunyili.

Ya kuma ce, dukkan wasu kashe-kashe a yankin ‘yan IPOB ne suke aikatawa cikin rashin tausayi.

Uche Mefor, barrantaccen mataimakin shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, ya zargi kungiyar da kisan Dakta Chike Akunyili a jahar Anambra, ShaharaReporters ta rawaito.

Dakta Chike shine mijin marigayi Dora Akunyili, tsohuwar Ministar Yada Labarai da Sadarwa kuma Darakta-Janar na Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC).

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun harbe Dakta a ranar Talata 28 ga watan Satumba yayin da yake dawowa Enugu daga Onitsha, inda ya halarci lacca na tunawa da aka shirya don girmama marigayiyar matarsa.

Kwanan nan, an yi kashe-kashe a yankin Kudu Maso Gabas da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka aikata.

Gwamnati da wasu mutane na zargin haramtacciyar kungiyar IPOB da reshen mayakan ta wato ESN da hannu a kashe-kashen, zargin da kungiyar ta IPOB ta sha musantawa.

Kisan na Dakta Chike na da alaka da ‘yan kungiyar IPOB wanda shugabansu ke tsare a hannun gwamnatin tarayya, amma kungiyar ta karyata, inda ta ce kisan nasa na da alaka da ‘yan siyasa.

Da yake mayar da martani kan kisan gillar da aka yi wa Akunyili, Mefor ta shafinsa na Facebook a ranar Alhamis 30 ga watan Satumba ya zargi IPOB da karkacewa daga “gwagwarmayar ‘yanci” zuwa kisan ‘yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba.

Da yake tabbatar da irin barnar aikin ta’addanci na IPOB, Mefor ya ce, IPOB ne ke da alhakin kashe-kashe a yankin ciki har da:

“Na baya-bayan nan shine kisan gilla da aka yiwa Dr Akunyili.”

Ya kuma bayyana babban abin kunya ne ga manya a yankin kudu maso gabas su gagara ambatan sunan ‘yan IPOB a matsyain ‘yan ta’addan da suke aikata munanan kashe-kashe a yankin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here