Kada ku Zargi Kowa Sai Gwamnatin Tarayya Idan ƙungiyar mu ta Sake Rufe Makarantu – ASUU

 

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta kasa, ASUU, ta bayyana cewa yadda gwamnati ke jan kafa wajen cika alkawari ka iya jawo wani sabon yajin aiki.

Kungiyar tace watanni 9 kenan da suka shuɗe bayan janye yajin aiki, amma gwamnati ta gaza cika alkawarinta.

ASUU ta yi kira ga yan Najeriya kada su zargi kowa sai gwamnatin tarayya idan ƙungiyar ta sake rufe makarantu.

Abuja – Ƙungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU), sashin Abuja, ta zargi gwamnatin tarayya da kokarin tilasta mata sake shiga wani sabon yajin aiki a faɗin ƙasa, kamar yadda Leadership ta rawaito.

Kungiyar tace rashin aiwatar da sabon tsarin biyan albashi na UTAS, rashin sakin kuɗin alawus na EAA, da sauransu da FG ta yi ka iya tilastawa malaman sake shiga yajin aiki.

ASUU tace ba zata tabbatar da cewa ba zata sake shiga sabon yajin aiki ba nan gaba duba da yadda gwamnati ta ɗauki aiwatar da yarjejeniyar MoA da aka cimma a baya.

Shugaban ASUU reshen ɓangaren Abuja, Dakta Salahu Muhammed Lawal, shine ya bayyana haka a wurin taron manema labarai a Abuja, ranar Talata.

Shin laifin waye idan ASUU ta sake shiga yajin aiki?

Dakta Lawal ya yi kira ga yan Najeriya da kuma iyayen da ƴaƴansu ke karatu a jami’o’in gwamnati da kada su zargi kowa sai FG kan sakamakom da ka iya biyo baya idan ba’a aiwatar da MoA ba.

Yace:

“Idan baku manta ba kungiyar mu ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar MoA tare da gwamnati, wanda ya sa muka janye yajin aiki a watan Fabrairu, 2021.”

“Amma watanni 9 sun shuɗe babu wani labari, ASUU na kira ga gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta ɗauka, ta aiwatar da tsarin biyan albashi na malaman jami’o’i UTAS.”

FG ta saba mana haka – ASUU

Bugu da kari, Dakta Lawal yace gwamnati ta saba yiwa ƙungiyar haka, taki cika alƙawarin da ta ɗauka, matakin dake jawo sake tsunduma wani sabon yajin aiki.

Saboda haka, muna bukatar gwamnatin tarayya ta gaggauta aiwatar da daftarin yarjejeniyar MoA da aka cimma tsakanin ɓangarorin biyu ranar 7 ga watan Fabrairu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here