KYPC: Ziyarar Gani da Ido
A kokarinta na wayar da kan al’uma don Samar da Shugabanci da Shugabanni nagari, a jahar Kano, kungiyar Youth Promotion Council (KYPC) a karkashin Shugabancin Comrade Idris Ibrahim Unguwar gini, ta fito da wani tsare na bibiya tare Kai ziyarar gani da Ido ga mazabun tarayya Dake fadin jihar Kano Dan gani tare da tabbatar da cewa wakilan tarayya na aiwatar da nagartattun ayyuka.
A sakamakon haka ranar lahadi 16/05/2021 kungiyar KYPC tare da hadin gwiwar MPCP sun Kai ziyarar gani da ido mazabar tarayya ta Dawakin kudu da warawa, inda Dan majalisar tarayya Hon Mustapha Bala Dawakin da kansa ya zaga da su don gani da Ido, ziyarar da ta dauki tsahon yini guda, ga Jeri wasu daga cikin ayyukan da ya aiwatar.
ILMI:
1.Dan majalisar ya Samar gurbi tare gina matsugunin da dindin ga offishin shiyya na hukumar jarabawar NECO, ginin da ake sa ran zai kunshi Zonal office da Kuma State office ginin ya kunshi ofisoshi, dakin na’ura Mai kwalwa.
2. Ya Samar da gurbi tare da Gina cibiya/reshen makarantar koyon harkokin sufuri ta tarayya ( National institute of Transport Technology),Wanda zai kula da shiyar jihohin Kano,Zamfara,jigawa,sokoto,kebbi,katsina da Kaduna, ginin da ke dauke da dakunan karatu, workshops guda 7, dakunan kwanan dalibai, gidan Shugabannin cibiyar,filayen Wasa da Kuma dakin inji Mai kwakwalwa da Kuma wajen gyaran motoci na zamani.
3. Ya Samar da gurbi ga budaddiyar jami’an (open University) Wanda a fadin Nigeria ba Mai girman sa, a kwai dakunan karatun dalibai, dakin inji Mai kwakwalwa Wanda zai ba damar a dinga rubuta jarabawar shiga jami’an (jamb), gidajen Shugabannin cibiyar, dakin jarabawa.
4. Ya Samar da cibiyar gyaran jarabawa (centre for remedial studies) ita ma dauke da dakunnan karatu, cibiyar inji Mai kwakwalwa da ofishin gudanarwa, wadda za’a dinga gudanat da karatun ta karkashin COC kumbotso.
Read Also:
5.Ya Samar da makamantan gaba da firamare (Secondary school) wacce aka sawa sunan marigayi hakimin Dawakin kudu Alh.Yusuf Bayero Wanda take dauke da ajujuwa, dakin karatu(library), dakin gwajegwaje (laboratories), kyaukykyawan mahalli San Nan an hada musu fitilun masu amfani da hasken Rana (solar panels).
6. Ya Samar da tarin ajujuwa guda dari uku a fadin mazabar Masa.
7. Yana ba da tallafin karatu ga Dalibai masu karantar fannin lafiya a jami’oi musamman’ya’ya mata (100% schoolarship to medical students).
TITINA:
1.Ya Samar da titina a cikin fadin garin Dawaki (township roads) tare da magudanan ruwa masu inganci.
2. Ya Samar da titina masu tsahon kilo mita biyu ga garuruwan da dama a mazabar sa.
3. Ya Samar da titi da ya hada garin Dawakin da garin mariri da Kuma titin Maiduguri.
LAFIYA:
1. Ya aiwatar da Gyara tare da Samar da cibiyar karbar haihuwa tare da kayan haihuwar na zamani (maternity centre) wacce aka hada da na’ura Mai bada hasken rana ( solar panels).
2. Ya Samar da asibiti Mai gado 51 tare da cibiyar karbar haihuwar ta zamani a garin warawa waccea a ka hada ta da na’ura Mai bada hasken Rana ( solar panels).
3. Lokaci-lokacin ya na daukan nauyin sansanin duba Marassa lafiya( medical outreach) wadda cibiyar lafiya ta azare (Federal medical center)da asibitin Mallam Aminu Kano kan gudanar,musamman Dan duba idanu da Kuma aikin cutar kaba.
NOMA:
1. Ya Samar da rijiyoyin ban ruwa na zamani sama da guda 2000(tubes well).
2 . Ya Samar da kayyan aikin gona tare da taki.
3. Ya samar da injinan ban ruwa kyauta ga manoma.
RUWA:
1.Ya Samar rijiyoyin tuka-tuka da masu amfani da hasken Rana guda 30.
FITILA.
Ya Samar da fitilun masu amfani da hasken rana a kan titinan garin Dawaki dama wasu tsangayu.
AYYUKAN DA BAA GAMA BA:
1. Ya samar fa fill domin Gina gidajen zamani masu bene guda 250 a bisa tsarin (FHS) don sawwake was ma,’aikata.
2.Ya samar da damar Gina ma’aikatar kyankyasar kana Nan masanaantu ta sheda Science and technology complex karkashin ma’aikatar Gwamnatin tarayya dake Abuja.
Bugu da Kari ya koyar da Mata 2500 sana’oi dabam-dabam, ya rarraba kayan sana’oin dogaro da Kai Kamar keken dinki, injin taliya.
Tijjani Sarki
For KYPC