Ko Kaɗan Zulum bai Cancanci Sake Komawa Kan Kujerar sa ba – Ɗan takarar NNPP

 

Ɗan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a zaɓen gwamnan jihar Borno ya caccaki gwamnan jihar, Babagana Zulum.

Dr Umar Alkali ya bayyana cewa gwamnan ko kaɗan Zulum bai cancanci sake komawa kan kujerar sa ba.

Ɗan takarar ya kuma zargi jam’iyyar APC a jihar da tafka maguɗin zaɓe a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata.

Jihar Borno- Ɗan takarar gwamnan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Borno, Dr Umar Alkali, ya bayyana cewa gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum, bai cancanci ya koma kan kujerar sa ba.

Ɗan takarar ya bayyana gwamnan a matsayin fankan ba kilishi domin babu wani abin a zo a gani da ya taɓuka a jihar.

Dr Umar Alkali ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise Tv ranar Laraba.

“Mutane a waje suna kallon Zulum a matsayin ɗaya daga cikin gwamnonin da suka fi kowa aiki, amma mu mutanen jihar Borno, muna kallon sa a matsayin gwamnan da yafi kowa rashin taɓuka abin kirki a tarihin jihar mu.” Inji shi

“Mun ƴan jihar ne mun san dukkanin abinda ke gudana a jihar, babu wani abu ɗaya tilo na cigaba a jihar, ba wai batun kawai gina gadoji bane.”

“Mutanen jihar Borno suna rayuwa ne cikin ƙangin talauci, ba su buƙatar gadar sama, satin da ya wuce na je sansanin ƴan gudun hijira a Bama, an ajiye mutane a wajen kamar dabbobi, ba tsaftataccen ruwa ba asibiti ba makaranta a wajen.”

Ɗan takarar ya bayyana cewa idan aka zaɓe su, za su mayar da hankali kacokan wajen yin ayyukan da zasu amfani rayuwar al’umma.

Ya Zargi APC da yin maguɗin zaɓe a jihar

Da yake tsokaci kan zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata, Dr Alkali Usman, ya zargi jam’iyyar APC da yin ƙarfa-ƙarfa wajen murɗe sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar.

Yace gwamnatin jihar tayi amfani da ƙarfin mulki wajen ganin ta tauye sakamakon zaɓen jihar, inda yace jam’iyyar su ta NNPP ta samu ƙuri’u sosai a jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here