Gwamna Zulum Yayi Hayar Jirgin Sama Domin Mika Hafan Soja Asibiti a Abuja Daga Borno
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya dauka shatar jirgin sama kacokan don a kai sojan da ya samu raunika Abuja don ganin likita.
An gano cewa, Manjo Garba ya samu miyagun raunika bayan arangama da ‘yan ta’adda amma jirgin kasuwa ya ki daukarsa saboda halin da yake ciki.
Kwatsam suka ci karo da Zulum a filin jirgi, wanda ya jingine tafiyar da zai yi inda ya nemi jirgin haya wanda ya dauka Garba kuma yayi masa rakiya har Abuja.
Maiduguri, Borno – Babagana Zulum, Gwamnan jihar Borno, yayi hayar jirgin sama domin mika wani hafsan soja asibiti a Abuja daga Borno.
Kamar yadda jaridar TheCable ta bayyana, hafsan sojan mai suna Manjo Garba, ya samu miyagun raunika daga harsasai yayin da suka yi fito na fito da ‘yan ta’addan Boko Haram a Wajiroko dake Damboa a jihar Borno.
Wallafar ta sanar da cewa, Garba wanda ke asibitin Maimalari, an bashi damar ganin likitansa dake Abuja.
Zagazola Makama sun wallafa cewa, sai dai an hana shi hawa jirgin kasuwa saboda halin da yake ciki.
Read Also:
“Sakamakon hakan, ya kwantar da hankalinsa inda ya yi yunkurin komawa asibitin tare da jiran jirgin soja na gaba da zai tashi zuwa Abuja.
“Kwatsam sai ga Gwamna Zulum zai tafi Abuja kuma suka ci karo da sojan a filin jirgin sama. Bayan ganin halin da yake ciki sai ya tsaya duba jikinsa.”
– Wallafar tace.
Zulum ya gane halin da sojan ke ciki
“A yayin gaisawarsI ne ya gane halin tashin hankalin da sojan ke ciki. An sanar masa masu jirgin sun ki tafiya dashi saboda halin da yake ciki.
“Sabo da tafiya a jirgin ‘yan kasuwa, Gwamnan ya tabu da halin da sojan ke ciki da yadda jirgin ‘yan kasuwa ya ki daukarsa, sai ya yanke hukuncin bashi taimako.”
Gwamna yayi hayar jirgi kacokan
A take sai Gwamnan yayi hayar jirgin sama wanda ya dauka Garba inda ya dire shi har Abuja.
“Ya ajiye shirinsa na tafiya da jirgin ‘yan kasuwan inda yayi hayar jirgi aka dauka sojan tare da rakiyarsa aka kai shi Abuja.”
– Wallafar tace.
A watan Augustan 2021, Faruk Yahaya ya kaddamar da tafiya a jirgin sama daga sansanin sojin sama na Maiduguri ga sojoji da hafsoshin da suka samu hutun zuwa ganin iyalansu.
Shugaban sojin kasan a lokacin ya tabbatar da cewawannan cigaban wani kokari ne na tabbatar da walwalar sojin dake kai kawo daga arewa maso gabas zuwa sauran sassan kasar nan.