Ambaliyar Maiduguri: Gwamna Zulum ya Kafa Kwamitin Rabon Kayan Tallafi

 

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kafa kwamitin rabon kayan tallafi ga mutanen da iftila’in ambliya ya shafa a Maiduguri, babban birnin jihar.

Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Bukar Tijjani ya fitar, gwamna Zulum ya ce kwamitin mai mamboi 35 zai kunshi wakilai daga hukumomi da dama da suka haɗa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da takwararta ta ICPC da kuma hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa masu ba shi shawara da wakilan hukumar raya yankin arewa maso gabas (NEDC), ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa da ma’aikatar kudi da ta mata da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) da sauransu.

Gwamna Zulum ya buƙaci mambobin kwamitin da su jajirce wajen sauke nauyin da aka ba su da kuma yin gaskiya.

“Za mu tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗin ta hanyar da ya dace, za mu tsaya mu ga tallafin ya kai ga mutanen da aka yi domin su,” in ji Zulum.

Ya ce gwamnatin jihar za ta tabbatar da ganin an sake gyara wurare kamar asibitoci da hanyoyi da kuma gadoji.

Mutane da dama dai, musamman masu hannu da shuni suka bayar da tallafin kuɗaɗe da kuma kayan abinci zuwa ga waɗanda ambaliyar Maiduguri ta shafa.

Ya ce sun samu karɓar tallafi da ya kai naira biliyan 4.4 zuwa cikin asusun tallafin jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here