Gwamna Zulum Zai ɗauki Malamai 5,000 Aiki da Dawo da Karatun Yamma
Gwamnar jihar Borno, Babagana Zulum ya ce za a dauki malamai 5,000 aiki don fara karatun firamare da sakandare da rana domin magance matsololin cunkoso da kuma rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Maiduguri yayin jawabinsa na farko bayan rantsar da shi karo na biyu.
Ya ce : “Duk da cewa mun gina sabbin makarantu masu girman gaske tare da fadada makarantun da ake da su da sabbin ajujuwa kusan 1,000, amma har yanzu muna fuskantar matsalar cunkoso a ajujuwa, kuma muna fama da matsalar da dubban yara da ba sa zuwa makaranta”
Read Also:
“Ina mai farin cikin sanar da cewa nan ba da jimawa ba jihar Borno za ta fara tsarin makarantun firamare da sakandare na rana. Na nada kwamitin aiwatarwa da zai tsara hanyoyin da za a fara karatun makarantun la’asar, kuma zai tantance makarantun gwajin da za a zabo daga wasu manyan makarantunmu na Maiduguri da ke da lantarki.”
Zulum ya bayyana cewa bullo da tsarin karatun na yamma zai bukaci karin ma’aikata, don haka ya umurci ofishin shugaban ma’aikata da ya zakulo wasu kwararrun ma’aikatan da a halin yanzu ba sa aiki a sakatariyar gwamnati, wadanda za a horar da su kan sanin makamar aikin.
Gwamnan ya kuma ce za a dauki matakan tsaro domin tabbatar da samun nasarar makarantun na yamma, yana mai cewa a wasu lokutan ana iya daukar darasi har zuwa farkon dare.
Zulum ya ce za a sake bullo da wasu matakai kamar jarrabawar gwaji da ake kira ”Mock” da Ingilishi a makarantun sakandare tare da kafa cibiyoyi daukar jarrabawa masu inganci ta yadda gwamnati za ta iya gano baiwa da fasihar yaran.