Gwamna Zulum ya Gabatar wa Majalisar Dokokin Borno Sunayen Mutane 20 da Zai Naɗa Sabbin Kwamishinoni

 

Gwamnan Babagana Umaru Zulum ya gabatar wa majalisar dokokin Borno sunayen mutum 20 da zai naɗa kwamishinoni.

Zulum ya sallami mambobin kwamitin zartarwan jihar ne a watan da ya gabata yayin da APC ta fara gudanar da zaɓen fidda yan takara na zaɓen 2023.

Sabuwar tawagar mutanen da Zulum ya zaɓo sun kunshi da yawa daga cikin tsofaffin kwamishinonin da ya sallama a baya.

Borno – Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya gabatar da sunayen sabbin kwamishinoni 20 da yake son naɗawa ga majalisar dokokin jihar don tantance su, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya rushe mambobi 20 na majalisar zartarwarsa a watan da ya gabata lokacin da jam’iyyar All Progressive Congress (APC) ke gudanar da tarukan zaɓen fidda yan takararta na zaɓen 2023 da ke tafe.

Yayin da yake gabatar da jerin sunayen sabbin kwamishinonin ga majalisar dokokin Borno jiya Talata, gwamnan ya ce wasu tsaffin kwamishinonin sun samu shiga cikin sabuwar tawagar.

Sunayen mutum 20 da Zulum ya gabatar wa majalisa

Jaridar da tattaro cewa daga cikinn sunayen da Zulum ya gabatarwa majalisa, mutum uku ne sabbi yayin da sauran 17 suna cikin tsofaffin da ya sallama a baya.

Sabbin da gwamnan ya zaɓa sune Farfesa Mohammed Arabi, Pogu Lawan Chibok da kuma Ali Bunu Mustapha.

Sauran mutum 17 daga cikin 20 da suka rasa aikin su baya, waɗan da suka sake shiga sabuwar tawagar sun haɗa da, Mustapha Gubio, Adamu Lawan, Yerima Saleh, Lawan Wakilbe, da Kaka Shehu Lawan.

Sai kuma Abacha Ngala, Isa Haladu, Sugum Mele, Zuwaira Gambo, Tijjani Goni, Babagana Malumbe, da kuma Yerima Kareto.

Saina Buba, Yuguda Saleh, Buba Walama, Abubakar Tijjani da kuma Babakura Abba Jato duk suna cikin tsofaffin kwamishinonin da Allah ya sake ci da su a sabbin da Zulum ya gabatar wa majalisar dokokin Borno.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here