Gwamna Zulum Ya ɗauki Nauyi Karatun Marayu 5,361 Kyauta

Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya jagoranci sanya marayu makaranta a garin Monguno.

Zulum wanda ya ɗauki bayanan marayun da kansa, ya ɗauki nauyin basu duk abinda ake bukata kyauta.

Hakazalika, Zulum ya yi alkawarin sanya wasu yara makaranta waɗanda iyayensu suka bukaci hakan.

Borno – Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ranar Laraba a garin Monguno, ya jagoranci saka marayu 5,361 da rikicin Boko Haram ya kashe iyayensu a makaranta.

Zulum wanda dakansa ya jagoranci ɗaukar bayanan Marayun, ya shafe kwanaki biyu yana gudanar da aikin.

Wannam na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnan ya fitar a shafinsa na kafar sada zumunta Facebook.

Marayun waɗanda shekarunsu ke tsakanin 7 zuwa 13 za’a ɗauki nauyin kayan makarantarsu, kayan karatu da kuma basu abinci duk kyauta.

An yiwa marayun rijistar makaranta a gaban makusantansu, waɗanda suka bada bayanai game da su da suka haɗa da garuruwan da suka fito da kananan hukumominsu.

Shin su kaɗaine marayun da gwamnati zata ɗauki nauyi?

Waɗanda aka sanya makarantar wani bangare ne na yara 50,000 da rikicin Boko Haram ya maida marayu ko aka nemi iyayen su aka rasa sanadin harin yan Boko Haram tun shekarar 2009.

Wasu iyaye sun nemi Zulum ya haɗa da ‘ya’yansu

Duk da cewa shirin na marayu ne kaɗai, amma wasu iyaye a garin sun kawo yayan su, inda suka nemi a sanya su a makaranta.

Bayan wannan bukata ta wasu iyaye ne, Gwamna Zulum ya yi musu alkawarin zai duba kuma ya amince nan gaba.

Gwamna Zulum yace:

“Muna kira ga makusantan waɗannan marayu da aka sanya a makaranta da su taimaka mana wajen sanya ido akan yaran, domin tabbatar da suna zuwa yanda ya kamata.”

Yayin gudanar da aikin saka marayun makaranta, Zulum ya samu taimakon kakakin majalisar dokokin jahar, Abdulkarim Lawan, kwamishinoni da kuma manyan jami’an gwamnati.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here