Ambaliyr Maiduguri: Gwamna Zulum ya ƙaddamar da Aikin Raba Tallafi ga Mutane Miliyan Biyu
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ƙaddamar da aikin raba tallafi ga mutane fiye da miliyan biyu da ambaliyar Maiduguri ta shafa.
Magidanta 5,235 ne a yankin Gwange 1 suka fara amfana da tallafin da gwamnan ya ƙaddamar ranar Talata.
Gwamnan ya ce gidajen mutum 587 da suka amfana daga tallafin sun rushe baki ɗaya inda magidanta 2,365 kuma gidajensu suka samu ƴar matsala sannan mutum 2,283 kuma nasu gidajen sun ɗan taɓu.
Read Also:
Gwamnan ya ce tallafin zai kasance hawa-hawa, inda waɗanda suka samu ƴar matsala a gidajen nasu za su samu naira dubu 100 da ƙaramin buhun shinkafa da wake da tabarmi da barguna da gidan sauro.
Sauran kuma waɗanda ambaliyar ko dai ta rushe musu gida baki ɗaya ko kuma ta illata shi za su karɓi abin da ya dace asarar da suka yi.
Farfesa Zulum ya kuma kara sanar da jama’a cewa yawan kuɗin tallafin da suka samu daga gwamnatoci da ɗaidaikuwar al’umma sun kai naira biliyan 7.5 ya zuwa lokacin ƙaddamar da rabon tallafin ranar Talata.
A ranar Litinin ne dai gwamnan ya ƙaddamar da kwamitin mutum 32 da zai ɗauki alhakn yin rabon tallafin ga al’ummar da ambaliyar ta shafa, inda a lokacin ya sanar da cewa an yi wa al’ummar alƙawarin gudunmowa da ta kai yawan naira biliyan 13,195,500,000.