Tsaro: Gwamna Zulum na Taro da Gwamnonin Jahohin Tafkin Chadi
Gwamnonin jahohin yankin Tafkin Chadi na gudanar da taro a birnin Yaounde na ƙasar Kamaru, don yin nazari kan harkokin siyasa da tsaro da kuma ayyukan jin ƙan ɗan’adam a yankin.
Taron dai na ƙoƙarin shaida ɓangarorin da gwamnonin ya kamata su ƙarfafa haɗin-gwiwa da tallafawa juna baya ga musayar ilimi tsakanin masana a faɗin duniya da takwarorinsu na ƙasashen yankin.
Read Also:
Yankin wanda ya haɗa iyakar ƙasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi – ya tagayyara sakamakon ɗumbin matsaloli ciki har da ƙaruwar taɓarɓarewar tsaro da janyewar gawurtaccen tafkin Afirka.
Lamarin dai ya shafi hanyoyin neman abinci ga ɗumbin mutane.
Mahalarta tarona sun hada da Zulum daga Borno da Issa Lamine na Diffa a Jamhuriyar Nijar; Midjiyawa Bakari na Arewa mai nisa a Kamaru; Abate Edii Jean Yankin Arewa a Kamaru.
Akwai kuma Mahamat Fadoul Mackaye na yankin Lac a Chadi da Amina Kodjyana Agnes – Hadjer Lami ita ma daga Chad.
Akwai kuma gwamnonin Adamawa da Yobe na arewa maso gabashin Najeriya.