Zuwa Gidan Yari Wani Bangare ne na Rubutun Rayuwata – Sanata Orji Kalu

 

Sanata Orji Uzor-Kalu ya bayyana cewa shiga gidan yari wani abu ne da ya canza masa rayuwa.

Tsohon gwamnan na jahar Abia ya ce yana daga cikin kaddararsa shafe wani lokaci a gidan yari.

Kalu yana mayar da martani ne game da kalaman abokan hamayyarsa na siyasa da suke yi masa ba’a kan tsare shi na wata 6 Tsohon gwamnan jahar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa ba ya jin kunyar zaman watanni shida da yayi a kurkuku.

Kalu wanda shine sanata mai wakiltar yankin Abia ta Arewa a yanzu ya yi wannan tsokaci ne a wurin kamfen din Mascot Uzor Kalu, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a mazabar Aba ta Arewa / ta Kudu a majalisar wakilai.

Mascot kane ne ga Orji, wanda kuma shi ne babban bulaliyar Majalisar Dattawan Najeriya a halin yanzu.

Sanatan yana mayar da martani ne ga kalaman da aka alakanta da Gwamna Okezie Ikpeazu da Sanata Enyinnaya Abaribe, shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa.

Kwanaki mutanen biyu sun yi wa Kalu ba’a inda suka ce bai farfado daga halin da ya shiga a gidan yari ba bayan da ya tabbatar da cewa hanyoyin da ke Abia gwamnatin tarayya ce ta biya su ko kuma hukumar ci gaban Neja Delta.

Jaridar The Cable ta ruwaito Kalu yana cewa: “Yanzu karfe 10 na dare kuma ina nan tare da ku, shin gwamna ko Abaribe za su iya zuwa nan?

Wannan shine dalilin da ya sa a jagoranci, dole ne ka kasance tare da mutanen da kake jagoranta.

“Amma ba su fahimci wannan fasaha mai sauki ba, duk ayyukan da suke ikirarin suna yi duk a rediyo suke, ba komai a kasa.

Annabi Yusuf ya shiga kurkuku, hatta Obasanjo ma ya shiga kurkuku. “Zuwa gidan yari wani bangare ne na rubutun rayuwata kuma ina godiya ga Allah da ya yarda da hakan.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here