Zuwaira Hassan: Tsohuwar kwamishinar Lafiya ta Jihar Bauchi ta Rasu

Allah ya yi wa tsohuwar kwamishinar lafiya ta jihar Bauchi, Dr. Zuwaira Hassan rasuwa.

Zuwaira ta rasu a hatsarin mota a safiyar yau Litinin, 23 ga watan Nuwamba, a hanyarta na dawowa Bauchi daga Plateau.

Marigayiyar ta rasu ta bar mijinta na sunnah da yara uku, za a yi jana’izarta da karfe 1:30 na rana.

Shugabar sashin likitoci ta kwalejin likitanci, asibitin koyarwa na jamiar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi, Dr. Zuwaira Hassan ta mutu a hatsarin mota.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa hatsarin ya afku ne a safiyar yau Litinin, 23 ga watan Nuwamba a kauyen Zaranda, kimanin kilomita 36 daga garin Bauchi.

Dr. Zuwaira ta kasance kwamishinar lafiya a gwamnatin baya ta Mohammed Abubakar. Ta rasu tana da shekaru 46 a duniya.

An tattaro cewa za a sallaci gawarta da misalin karfe 1:30 a babban masallacin asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa.

Daga nan za a binne ta a makabartan Musulmai da ke a hanyar Gombe Road daidai da koyarwar addinin Islama.

Wani kanin marigayiyar, Garkuwa Adamu, jami’in hulda da jama’a na hukumar tsaro ta NSCDC reshen Bauchi, wanda ya tabbatar da lamarin a wayar tarho, ya bayyana cewa lamarin mutuwar ya sanyasu cikin dimuwa.

Ya ce: “Eh, da gaske ne, ta mutu a safiyar yau a wani hatsarin mota a kauyen Zaranda a hanyarta na dawowa Bauchi daga Jos, jihar Plateau.

“Su uku ne a cikin motar lokacin da lamarin ya afku. Abun bakin ciki ne sosai ka tashi da mutum yanzu sannan anjima ace babu shi, abun bakin ciki ne matuka.

“Tana da kwazon aiki sosai da jajircewa a kan aikinta. Za mu yi kewarta sosai.”

Da aka tuntube shi, Shugaban hukumar hana afkuwar hatsarurruka, Yusuf Abdullahi, ya ce baida cikakken labari game da hatsarin tukuna.

Ta rasu ta bar mijinta da yara uku.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here