2023: Ana Ikirarin Wasu Gwamnoni Sun yi wa Jonathan Tayin Shugaban Kasa

Wani rahoto ya yi ikirarin cewa yan siyasa a APC na kokarin neman dan takarar Shugaban kasa da ya kamata gabannin zaben 2023.

Wata jaridar kasar ta ruwaito cewa ziyarar da gwamnonin APC suka kai wa tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan na siyasa ne.

Ziyarar da gwamnonin na APC suka kai masa ya kuma haifar da rade-radin shugabancin Jonathan a 2023.

Wani rahoto da ya billo ya yi ikirarin cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na zawarcin tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan, domin ya fito takarar Shugaban kasa a inuwarta a 2023.

Rahoton wanda jaridar This Day ta kawo ya yi ikirarin cewa wasu shugabannin jam’iyyar na matsawa tspohon Shugaban kasar a kan ya duba yiwuwar amsa tayin.

Jaridar ta bayyana cewa wata majiya wacce ta nemi a boye sunanta ta ce gwamnonin APC wadanda suka ziyarci Jonathan don taya shi murnar cika shekaru 63, sun yi amfani da taron wajen yi masa tayin kujerar shugabancin kasar.

Rahoton ya ci gaba da ikirarin cewa makusantan Buhari na goyon bayan yunkurin ganin Jonathan ya zama Shugaban kasa a 2023.

A cewar ikirarin, makusantan Buhari sun yarda cewa Jonathan ba zai cutar da ra’ayin kungiyarsu ba saboda haka shine ya cancanci karban mulki idan aka mika ta kudu.

Wata majiya a sansanin Buhari wacce bata so a bayyana ta tace:

“Ya mika mulki cikin lumana sannan bai riki kowa ba saboda haka ba zai zama barazana ga ra’ayin arewa ba.”

Sai dai, a baya Jonathan ya sha karyata cewar yana da ra’ayin takarar Shugaban kasa.
Tsohon Shugaban kasar ya bayyana arara cewa ya mayar da hankalinsa ne a kan gidauniyarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here