Yanda Tattalin Arzikin Nageriya ya Lalace a Mulkin Buhari – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce ya matukar girgiza da samun labarin cewa tattalin arzikin Nigeria ya sake karyewa.

Wannan shine karo na uku da tattalin arzikin Nigeria ya sake karyewa a karkashin mulkin Buhari.

Atiku ya ce lokaci ya yi da ya kamata shugaba Buhari ya bude kunnuwansa ya ajiye siyasa a gefe, ya saurari shawarwarinsu.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya wallafa sakon shawarwari ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bayan tattalin arzikin Nigeria ya sake karyewa a karo na uku.

“Zuciyata ta yi nauyi sakamakon samun tabbacin mun sake faɗawa ruwa a karo na biyu sanadiyyar mashasharar tattalin arziƙi, Najeriya ta sake faɗawa ƙangin tattalin arziki.

“Eh, tabbas annobar COVID-19 ita ce silar janyo wannan matsala, sai dai, da tuni mun kaucewa wannan hali ta hanyar ta amfani da basira gami da hangen nesa tare da tattala tattalin arziƙin mu.

“Tunda mai afkuwa ta afku, ba haƙƙin kowa bane tada jijiyar wuya akan batun. Dole mu maida hankulanmu kan nemo mafita. Najeriya na buƙatar nagartaccen shugabancin da zai ja akalarta zuwa hanyar farfaɗo da tattalin arziƙinmu.

“Ba zai yiwu mu naɗe hannayen muyi zuru ba. Dole mu ɗauki mataki ta hanyar gudanar da abubuwan da suka zama dole, wataƙila matakan su kasance masu zafi da raɗaɗi.

“Farawa da kasafin kuɗin da aka gabatarwa majalisa a ranar Talata, 8 ga watan Oktoba 2020, baya cikin tsari yanzu.

“Najeriya ba tada ma’adanai ko buƙatar kasafin alatu mai tsada irin wanda shugaban kasa ya gabatar.

“Ƙasa ta tagayyara, amma bata rushe ba. Duk da haka, idan muka cigaba da almubazzaranci, ko da abin da muke samu bai kai gejin da muke nema ba, ƙasar zata tashi daga tagayyararriya zuwa rusashiyar ko ɓallaliyar ƙasa.

“Saboda kaucewa hakan, akwai matakan da ya kamata gwamnati ta dauka cikin gaggawa.

“Wannan ya haɗar da soke tafiyar da ba ta gaggawa da hanzari ba, rage kudin ciyarwar shugabanni, hakura bushasha da jindaɗi, dakatar fita horo a ƙasashen waje, hakura da siyo sabbin ababen hawa da gyaran ofisoshi da kuma alawus ɗin da bana albashi ba da sauransu,” kamar yadda Atiku ya wallafa a shafinsa na tuwita.

Atiku ya ce lokaci ya yi da ya kamata shugaba Buhari ya bude kunnuwansa, ya saurari shawarwarin da ake bashi a kan hanyoyoyin gyara tattalin arzikin Nigeria ba tare da la’akari da banbancin jam’iyya ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here