APC: Gwamna Zulum ya Nemi a Mayar da Mulkin Kasa Zuwa Kudanin Najeriya a 2023

 

Gwamnan Borno Farfesa Babagana Zulum ya ce yana goyon bayan mulki ya koma kudu a 2023.

Zulum ya yi kira ga jam’iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) ta karrama yarjejeniyar da aka yi a baya na mayar da mulki kudu.

Gwamnan Borno ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis wurin kaddamar da wani littafi kan tsaro.

Gwamnan Jahar Borno, Babagana Umara Zulum ya nemi a mayar da mulkin kasa zuwa kudanin Nigeria a gwamnati mai zuwa a shekarar 2023, Channels Television ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin jawabin da ya yi wurin taron tsaro da habbaka tattalin arziki wurin kaddamar da littafin da tsohon shugaban NIMASA, Dakuku Peterside ya wallafa mai taken “Strategic Turnaround”.

Ya yi kira ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta karbi shawararsa ta amince da yarjejeniyar da aka yi a baya na cewa mulki zai koma kudu a 2023.

Gwamnan ya yi amfani da damar wurin danganta rashawa da gwamnatocin baya suka yi da Boko Haram.

Ya kara da cewa kuskuren da Nigeria ta yi ne ya janyo aka samu yan bindiga da ke adabar kasar.

Ya yi ikirarin cewa “Idan Nigeria ta yi koyi da wasu kasashen Afirka ta tallafawa kasashen da ke makwabtaka da ita, da an magance matsalar.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here