Kotu ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Barayi a Jahar Ondo

 

Bayan shekaru shida, kotu ta yanke hukunci kan barayi uku a jahar Ondo.

Yan fashin su shiga unguwa inda suka kwace wayoyi kuma suka tafi da babur.

Yanzu Alkali ya ce hukumar ta kashesu ta hanyar rataya An yankewa ‘yan uwa biyu, Sunday da Lucky Isaac, da wani dan babur, Ovie Nana, hukuncin kisa a ranar Juma’a kan laifin fashi da makami a jihar Ondo.

Alkali Yemi Fasanmi na babban kotun jihar ya tabbatar da laifi kan mutanen uku bayan kimanin shekaru shida ana Shari’a.

A ranar 11 ga Disamba, 2013, Sunday, Lucky da Ovie sun yiwa mazauna unguwar Bolorunduro fashi da makami inda suka kwashe dukiyoyi.

Masu laifin uku sun hada baki ne domin sace waya, kudi da wasu dukiyoyin mutanen.

Bayan damkesu a 2014, an gurfanar da su a kotu kan laifuka biyar.

A shari’ar da Alkalin ya yanke, ya bayyana cewa lallai ya gamsu da hujjojin da aka gabatar kan masu laifin kuma ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here