2023: Ku Soke Sunan Duk Dan Majalisar da Bai Muku ba – Ahmad Lawan Zuwa ‘Yan Najeriya

 

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya bukaci ’yan Najeriya da su yi waje da duk dan majalisar da bai yi musu ba a 2023.

Lawan ya soki masu kira da a soke majalisar dattawar saboda makudan kudaden da ake biyan sanatoci.

Ya ce soke majalisar za ta haifar da matsala na rashin tsari a kasar.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi gargadin cewa za a fada yanayi na rashin tsari idan har aka soke majalisar dattawa kamar yadda wasu ‘yan Najeriya suka bukata.

Maimakon haka, ya kalubalanci wadanda basu gamsu da sanatocin da ke majalisar ta tara ba da su yi waje da su a 2023 idan har sun san cewa basa son ganin fuskokinsu.

Lawan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamba, yayinda yake kaddamar da bude taron ma’aikatan gudanarwar majalisar tarayya da na hukumar ayyukan majalisar a Abuja.

Ya bayyana majalisar dattawa a matsayin mai tabbatar da daidaito wajen ganin an wakilci dukkanin yankunan kasar sabanin majalisar wakilai inda jihohi da suka fi yawan al’umma suka fi samun yawan wakilai.

Shugaban majalisar dattawan ya kuma soki sharhin wadanda ke neman a soke majalisar dattawan saboda kaso mai tsoka da sanatocin suke karba, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce kasafin kudin majalisar dokokin tarayya ya kasance kasa da kaso daya cikin dari na kasafin kudin kasar na 2021.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here