2023: ‘Yan Najeriya su Zaɓo Shugaban da ya Dace da Halin da Ake Ciki – Attahiru Jega
Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, yace kai shugabancin kasa wani yanki ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
Jega yace abinda ya fi muhimmanci shine yan Najeriya su zaɓo shugaban da ya dace da halin da ake ciki.
A cewarsa ko daga wane yanki ya fito indai yana da kwarewar da ake bukata to yan Najeriya su zabe shi.
Abuja – Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa tsarin mulkin karɓa-karba ba zai fitar da ƙasar nan daga kalubalen da ta tsinci kanta a ciki ba.
Jega yace wuka da nama na hannun yan Najeriya su zabi nagartaccen mutum wanda zai iya jagorancin kasar nan a 2023, kamar yadda the cable ta ruwaito.
Read Also:
Farfesa Jega ya yi wannan tsokaci ne yayin wata tattaunawa a cikin shirin kafar watsa labarai ta Arise TV ranar Litinin.
Waye ya dace da mulkin Najeriya?
Tsohon shugaban hukumar INEC, Jega yace:
“A halin da Najeriya ke ciki, muna bukatar nagartaccen mutum wanda yake da kwarewar zama shugaban ƙasa kuma ya fitar da ƙasar nan daga kalubalen da take ciki a yanzu.”
“Ko ya fito daga arewa, kudu, gabas ko yamma abinda yafi muhimmanci shine idan jam’iyyun siyasa suka tsaida ɗan takara daga kowane yanki ya fito, hukunci na hannun yan Najeriya.”
“Abinda ya kamata yan Najeriya su sani shine ya zama wajibi su natsu su tace sannan su zaɓi wanda ya dace da mulkin kasar nan.”
“Wannan maganar da ake ta tsarin mulkin karba-karba ba zai hitad damu daga ƙaƙani kayin da muke ciki a yanzun ba.”