Yadda Abdulrasheed Maina ya yi a Gaban Kotu
Tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, ya yanke jiki ya fadi a kotu.
Maina ya fadin ne yayinda ake ci gaba da shari’arsa a babban kotun tarayya da ke Abuja kan wasu tuhume-tuhume a yau Alhamis, 10 ga watan Disamba.
Zuwa yanzu da ake kawo wannan rahoton, tsohon shugaban hukumar fansho din bai farfado ba.
Abdulrasheed Maina, tsohon Shugaban hukumar fansho a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba, ya yanke jiki ya fadi a kotu a yayin shari’arsa, jaridar Tribune ta ruwaito.
Read Also:
Gwamnatin tarayya na shari’a da Maina a kan wasu tuhume-tuhume 12 da ta gabatar gaban wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja.
Tsohon Shugaban fansho din ya yanke jiki ya fadi ne da karfe 10:05 na safe lokacin da lauyansa, Anayo Adibe ke mika shari’arsa a gaban Justis Okon Abang.
Kafin ya yanke jiki ya fadi, lauyansa ya roki kotu a kan ta dage zaman domin bashi damar samun bayanai na zaman da kotu tayi domin ya samu damar shirya takardar babu kara da yake burin gabatarwa a madadin wanda yake karewa.
Sai da kotu ta dage zama ba tare da shiri ba domin ba jami’an hukumar gyara hali damar ba tsohon Shugaban fansho din kulawa.
A daidai lokacin kawo wannan rahoton da misalin karfe 10:30 na safe, Maina bai farfado ba