Yaƙin Iran: Kayan Abinci ya yi Tashin Gwauron Zabbi – MDD
Majalisar ɗinkin duniya ta ce farashin kayan abinci ya yi tashin da ya daɗe bai yi ba tsawon watanni shida da suka wuce, kuma akwai yiwuwar zai ci gaba da tashi idan yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da Isra’ila kan Iran ya ci gaba.
Read Also:
Babban jami’in tattalin arziki na hukumar kula da abinci da noma na Majalisar ya ce hauhawar farashin mai ne babban abin da za a ɗora wa alhakin karuwar farashin abincin zuwa yanzu, amma ya yi gargaɗin cewa katse samar da taki da wasu muhimman kayayyakin noma na iya ƙara ta’azzara lamarin.
Wakilin BBC ya ce kashi uku cikin ɗari na muhimman sinadaran da ake haɗa taki da su na bi ta mashigar Hormuz.
Ƙasashe da dama sun baiwa ma’aikata umurnin yin aiki daga gida,kuma sun ƙara farashin man fetir, sakamakon yadda hana wucewa ta mashigar Hormuz ya hana su shigar da mai da iskar gas cikin ƙasashensu.






